06
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayinda shahararren ɗan ƙwallon ƙafan duniya Christiano Ronaldo da takwaransa na ƙasar Portugal, Pepe ke shirin bankwana da buga wasa, ƴan wasan sun yi rashin nasara a hannun Faransa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar kofin Nahiyar Turai na 2024. Portugal ta sha kaye ne a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida bayan shafe mintuna 120 ba a samu wanda ya zura ƙwallo ba, inda daga baya Faransa ta doke ta da ci 5 da 3. Wannan ita ce gasar kofin ƙasashe ta ƙarshe da ƴan wasan biyu su ka sha alwashin ajiye aikinsu da…
