03
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ce Naira dubu ɗari huɗu a ke biyan sa duk wata a lokacin da ya ke shugabantar majalisar, saɓanin yadda a ke ta yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa maƙudan kuɗaɗe ƴan majalisu ke ɗauka a matsayin albashi. Dogara, wanda shi ne Kakakin a majalisa ta takwas (daga 2015, zuwa 2019), ya faɗi haka ne a zauren Majalisar da ke Abuja yayin jawabin fatan alkhairi ga ƴan majalisu a bikin satin majalisar ƙasa. Ya ce, kuɗin albashi da alawus ɗin da ya ke karɓa sun kai jimillar Naira miliyan…
