Babaji

5434 Posts

Safarar ƴan ƙunar baƙin wake a ka yi a Borno – Majalisar Wakilai

Daga FAROUK ABBAS Majalisar Wakilai ta ce tana zargin an yi safarar ƴan matan da suka ƙaddamar da ƙunar baƙin wake ne a jihar Borno wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama a ranar Asabar da ta gabata. Wakilin Majalisar, Ahmed Jaha a yayin magana kan wani batu na gaggawa game da al'amarin a Majalisar, ya ce bincike ya nuna cewa an yi hayar ƴan ƙunar baƙin waken ne daga wajen jihar Borno. Sannan, aikin tada bom ɗin wanda ya faru a Gwoza, an samu aƙalla mutane sama da 30 ne su ka rasa rayukansu tare da raunata sama…
Read More

Kotu ta buƙaci EFCC ta biya tarar Naira miliyan 3 kan shelanta kama matar Emefiele ba bisa ƙa’ida ba

Daga HAMZA RUFA'I Wata babbar kotu a jihar Lagas ta ce ba daidai ba ne shelanta neman kama matar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, Margaret da hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da laifukan da su ka shafi kuɗi (EFCC) ta yi. Mai Shari'a, Deinde Dipeolu ya faɗi hakan bayan da Magaret Emefiele ta shigar da ƙara kan EFCC da a bi mata haƙkinta inda kotun ta buƙaci hukumar da ta biya tarar Naira miliyan uku ga daƙile ƴancin matar. Magaret, ta shigar da ƙarar ne ganin yadda hukumar ta wallafa hotunanta a shafukan EFCC…
Read More

‘Yan sanda sun musanta rahoton fashewar bom a tashar lantarki ta Zungeru

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI 'Yan sanda a jihar Niger sun ƙaryata waɗansu rahotanni da ke cewa an samu tashin bom a tashar wutar lantarki na Zungeru da ke jihar Niger inda suka ce labarin ba gaskiya ba ne. Mai magana da yawun rundunar, Wasiu Abiodun ya ce labarin wanda ke yawo a kafafen yanar gizo, ƙanzon kurege ne da jama'a ya kamata su ƙi amincewa da shi. Abiodun, ya ce babu wani abu mai kama da haka a tashar lantarkin, don haka jama'a su yi watsi da shi. Ya kuma ƙara jaddada wa al'umma cewa, tashar tana gudana yadda aka…
Read More

Yadda ƴan bindiga suka yi garkuwa da mutune 20 a hanyar Ijebu-Ode zuwa Shagamu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ƙalla matafiya ashirin ne ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a kan babban titin Ijebu-Ode/Sagamu a ranar Lahadi, kusa da ofishin rundunar 'Yan sanda na birnin Ileshan da ke Shagamu. Kakakin rundunar Ƴan sandan yankin, Omolola Odutola ya ce an samu wani mutum da ake zargin ƴan bindigan sun harbe shi a gwiwa wanda a halin yanzu ya ke karɓar kulawa daga jami'an lafiya. Omolola ya ce sun tabbatar da batun garkuwa da mutanen inda ya ce suna ƙoƙarin gano inda ƴan bindigan su ke tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da…
Read More

Annobar Kwalara ta ɓarke a kurkukun Kirikiri, yayin da mutane 118 suka kamu a Katsina

Daga FAROUK ABBAS Kwamishinan lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce sun samu rahoton mutane 25 da ake zargin suna ɗauke da cutar ƙwalara daga gidan yarin Kirikiri. Hakan na zuwa ne bayan da hukumar kula da gidajen yari (NCS) ta fitar da bayanin cewa babu mai ɗauke da cutar a gidan kurkukun a makon da ya gabata. Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Umar ya ce sun ɗauki matakan kariya wajen ganin ba a samu ɓullar kwalara a gidan yarin ba. Sai dai, ma'aikatar lafiya ta jihar Lagos ta offishin jami'in hulɗa da jama'a, Tunbosun Ogunbawo ta…
Read More

Shugaba Tinubu ya yi wa Sanata Ali Modu Sheriff ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Daga Abdullahi Maitama Sani Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga tsohon gwamnan Jihar Barno, Sanata Ali Modu Sheriff kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Aisha. Za a gudanar da jana'izar Hajiya Aisha da ta rasu da shekaru 93 a gidansu na marigayi Galadima Modu Sheriff da ke kan hanyar Damboa a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno. Wata sanarwa da ta fito daga mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ta ce shugaba Tinubu na jajenta wa iyalan Sanatan kan babban rashin da aka yi mu su, yana mai rarrashin su tare da addu'ar fatan samun…
Read More

Rundunar ‘Yan sandan Abuja ta bayar da umarnin kama motoci marasa lamba

Daga EDITA Hukumar 'Yan sandan a birnin tarayya Abuja, ta bayar da umarnin kama duka motoci marasa lamba da ke yawo a faɗin birnin. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce kwamishin 'Yan sandan birnin, CP Benneth C. Igweh ne ya bayar da umarnin don kakkaɓe ayyukan ɓata-gari da ke fakewa da tuƙin mota suna cutar da al'umma. “Rundunar 'Yan sandan birnin Abuja ta damu matuƙa kan yadda ake tuƙa wasu motoci a birnin da lamba ɗaya kacal a jikinsu, da ma waɗanda ba su da lambar har fiye da lokacin da doka ta…
Read More

Yadda Sarki Sanusi ya karɓi baƙoncin Gwamnan Zamfara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya karɓi baƙoncin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawan a fadar Sarkin da ke Gidan Rumfa, wanda haka ke nuna ƙarfin alaƙar da ke tsakaninsu. Alaƙar tasu ta samo asali ne tun lokacin da Sarki Sanusi ke gwamnan babban bankin Nijeriya inda Dauda Lawan shi ne mai bashi shawara na musamman kan harkar bankin musulunci, wanda hakan ya taimaka wajen ƙirƙirar bankunan Ja'iz da TAJ da kuma Lotus gami da samar da tsare-tsare masu kyau a harkar banki. Dauda Lawan, ya yi abin a yaba a harkar banki a…
Read More

Gwamnan Kano ya buƙaci a binciki Ganduje kan rage kuɗaɗen tsofaffin ma’aikata

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roƙi a yi bincike kan zargin rage kuɗaɗen giratuti na tsofaffin ma'aikata ƙarƙashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje. A lokacin da ya ke jawabi a bikin ƙaddamar da zango ba biyu na biyan giratuti da na ma'aikatan da suka mutu, Abba ya ce akwai Naira biliyan 5 da aka rage na ƴan fansho mutum 4,000 cikin kuɗin wanda babu bayanai a kan su, don haka ya buƙaci hukumar da ke da alhaki a kai, ta yi bincike. Abba ya shawarci ƙungiyar ƴan fansho ta ƙasa (NUP), da ta shigar da…
Read More

Yadda wasu maƙiya su ka shirya bayanan ƙarya a kan ɗan jarida, Shuaibu Mungadi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shuaibu Mungadi ɗan jarida da ke aiki a gidan telebijin na Farin wata wanda ya tsinci kansa a wani mummunar yanayi, biyo bayan da wata kafa mai suna 'Zamfara News Letter' ta ruwaito cewa ana zarginsa da yi wa ƙawar ƴarsa ciki. Wannan labari ya ɗauki hankalin mutane kasancewar hakan abu ne da zai ɓata sunansa a cikin al'umma. Wani bincike da kafar ta yaɗa daga wasu ƴan siyasa waɗanda ke harin mutanen da suka saɓa da su wajen ra'ayi, ya ce, Mungadi ya ƙulla mummunar alaƙa da ƴar Maijidda Labaran wanda haka ta kai ga…
Read More