29
Jun
Daga BALA MUHAMMAD Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa, jami'an soji sun yi nasarar kama mutum 47 da ake zargi da satar turakun hanyar jirgin ƙasa a yanki Kakau Daji, a anguwar Ayaba da ke ƙaramar hukumar Chikun na jihar Kaduna. Mataimakin kakakin rundunar na yankin, Laftanal Musa Yahaya, ya ce jami'ansu sun kama waɗanda ake zargi ne a lokacin da su ke gudanar da wani zagaye a ranar 26 ga watan Yuni, 2024. Ya ce, waɗanda ake zargin sun cika motoci guda biyu da kayayyakin turakun hanyar yayinda aka kama su, sannan binciken su ya ce, wani mai suna…
