Dalilin tashin farashin wake a Nijeriya

Spread the love

Daga ABUBAKAR ABBA

Tsadar farashin wake ya jefa fargaba a zukatan mutane da dama a Nijeriya wanda har yanzu ke ci gaba da haifar da cece-kuce.

Jaridar ‘Leadership’ ta ruwaito cewa, tashin farashin waken na ƙoƙarin wuce gona da iri, wanda a tarihi ba a taba ganin irinsa a faɗin wannan ƙasa ba.

Har ila yau, manoman sun danganta tsadarsa da abubuwa da dama da suka shafi nomansa a Nijeriya.

Kungiyar manoman farin wake ta ƙasa (CFAN), ta sanar da cewa, ana ɗaukar mataki don lalubo mafita a kan wannan hauhawar farashi a faɗin wannan ƙasa.

Shugaban ƙungiyar na kasa reshen Jihar Kano, Malam Sale Maigari Tunfafi, ya sanar da cewa, ba wake kaɗai wannan hauhawar farashi ya shafa ba, sai dai kawai tashin farashinsa ne ya fi muni.

Ya sanar da cewa, ɗaya daga cikin abin da ya jawo tsadar shi ne; raguwar da aka samu ta masu yin nomansa a bara, wanda hakan ya yi nuni da cewa, wake na ɗaya daga cikin amfanin gona da ake girbewa a duk shekara.

Ya kara da cewa, kutsawar da makiyaya ke yi cikin gonakin da aka yi shuka, na haifar da lalacewar amfanin da aka shuka.

Kazalika, ya danganta hauhawar farashin kayan nomansa da haifar da raguwar yawan masu yin nomansa a faɗin wannan ƙasa.

Ya ci gaba da cewa, shigo da waken da wasu manyan dillalansa ke yi daga makwaɓtan ƙasashe, ya kara haifar da wannan hauhawar farashin nasa a Nijeriya.

A cewarsa, faɗuwar darajar Naira ma ta taimaka wajen haifar da tashin farashin nasa, wanda hakan ya sa wasu manyan dillalansa ke fitar da shi zuwa wasu ƙasashe, domin samun kuɗin musaya da kuma ƙazamar riba.

Ya bayyana cewa, tuni sun fara ɗaukar matakai domin noma waken da yawa, wanda hakan zai sa tsadar tasa ta ragu.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, farashin nasa ya haura Naira 200,000 duk loka ɗaya, wanda ake ganin shi ne mafi munin tashin farashinsa a shekaru da dama da suka gabata.

By Babaji