Daga DAUDA USMAN a Legas
An bayyana cewar rasuwar babban attajirin nan na jihar Legas, Marigayi Alhaji Ebetton Sardaunan Arab na jihar Legas rashi ne da ya girgiza dukkan al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas da kewayenta gabaɗaya.
Sarkin Musulmin Arab na jihar Legas Sultan Alhaji Jibirin Yaya ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron gudanar da addu’ar kwana bakwai da rasuwar ɗan uwansa Marigayi Alhaji Ebetton wanda ya gudana a harabar ƙofar gidan marigayin dake Ƙiri-ƙiri Road Apapa dake cikin garin Legas, inda Sarkin Musulmin na Arab a Legas ya cigaba da nuna irin rashin da al’ummar arewacin Nijeriya mazauna garin Legas da Kewayenta suka tafka dangane da rasuwar marigayin Alhaji Ebetton Galadiman Legas baki ɗaya.
Ya ci gaba da cewa haƙiƙa ‘yan Arewa mazauna jihar Legas da kewayenta gaba ɗaya sun tafka mummunar asara idan aka yi la’akari da irin gudummawar da marigayin yake ba ‘yan arewa mazauna Legas ta fuskar kariyar mutuncin su a da sauran al’amauran rayuwarsu ta yau da kullum.
Jibirin Yaya ya ce haƙiƙa ‘yan Arewa a Legas sun yi rashin gwarzon shugaba mai kyautata wa na ƙasa da shi a kowanne lokaci idan hakan ta taso. Ya ce a halin yanzu sai dai su cigaba da yin haƙuri tare da gudanar da addu’o’in Allah Ubangiji ya kawo masu wani a cikin zuri’ar marigayin wanda ko bai kai kamarsa ba ya samu ya kamanta yin a bubuwan da marigayin yake yi wa al’ummar Arewacin mazauna jihar Legas gaba ɗaya.
Injishi da fatan Allah ubangiji ya jikan dan uwan sa marigayi Alhaji Ebetton ya sanya al jannace