Daga MOHAMMED ALI a Gombe
Shugaban ‘yan Shi’a na Jihar Gombe dake Arewa maso gabashin Nijeriya, Sheikh Muhammad Adamu Abare, ya ja hankulan wasu shugabannin Afirka da Asiya da wasu ƙasashen Larabawa, da su yi hattara da dogaro da turawan yamma domin ba sa nufinsu da alheri.
Sheikh Abare wanda yake tattaunawa da ‘yan jaridu a horas ɗin shi a birni Gombe a makon jiya a saƙon shi na sallah layya da kuma batun rikicin Gabas ta Tsakiya, ya yi nuni da cewa, duk wani tayin taimako ko tallafi da Turawan yamma suke yi wa waɗannan ƙasashe da suke dogara da su, romon baka ce kawai domin su tsunduma su cikin bala’oi’ iri-iri amma ba domin wani alheri ba.
Shehin Malamin ya nuna takaici akan yadda ƙasashe suke dogara kacokan a kan mutanen da ya kira “muggan irin da basa nufin kowa da alheri illa su yasu kawai” yana mai lura da cewa, ƙasashen Afirka babu abin da aka rasa na cin arziki, amma shugabannin ta sun shagwabe ga neman taimako daga ƙasashen yamma.
Sai ya bada misali yadda ƙasashe kamar su Afganistan da Siriya da Iraƙi da Libiya da wasunsu suka shiga halin haula’in da har yau basu samu mafita ba, yana mai tambaya da cewa, “to ina taimakon da Turawan yamma suka yi musu in banda romon bakan karyayyakin da suke ta shelantawa duniya?”.
A kan rikicin Isra’ila da Falasdinu kuwa, Sheikh Albare ya ce yau kusan shekara ɗari Yahudawa suke ta muzgunawa al’ummar Falasɗinu kuma duniya na kallo ana ta ci gaba da azabtar da su kuma a cewar shi, duk aringizimo ce Turawan yamma suke yi na sasantawa domin sune suke fiffita Yahudawan a fakaice, suna ƙara musu ƙwarin gwiwwar ci gaba da kisan kiyashin da suke tayi akan Falasɗinawa waɗanda aka mamaye matsuguninsu.
Don haka, Albare sai ya yi kira ga Musulmin duniya masu tsoron Allah da su tashi tsaye suga an kawo ƙarshen yaƙin ƙare dangi da ake yi wa ‘yan uwansu Musulmi a Gabas ta Tsakiya, duk da dai a cewar shi, yanzu haka mutane a sassa daban-daban na duniya ciki har da wasu kasashen Turawa da Jamus da Faransa , suna ta zanga-zanga da yin tir da kisan kiyashin da Yahudawan keyi, kuma suna sharadin da a kawo karshen shi, abaiwa Falasɗinawa ƙasarsu.
Da ya juya a halin da Nijeriya ke ciki a yau, sai Shehin Malamin ya shawarci kowa da kowa-musulmai da kiristoci-da su tashi da yin adu’a ko Allah zai kawo karshen kuncin rayuwar da “yan kasar ke fama da shi sama da shekaru goma yau, yana mai karawa da cewa, babu wanda ya kai Ma’aikin Allah Rasulillahi (SWA) yin adu’a duk da irin gatan da Allah ya ba shi, “saboda haka, me ya sa muma ba za mu tinkari lamarin namu da adu’a ba?. Itace kawai mafita,” inji shi.
Sai ya taya musulmi farin cikin anyi Babban Sallah Lafiya, yana kuma shawara ga matasa da su guji fitintinu da shaye-shaye, su je su koyi ilmi ko kuma sana’a yana kuma fatan alheri ga Jihar Gombe da Nijeriya bakiɗaya.