’Yan bindiga sun fille kan ɗan tauri a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindiga sun fille kan wani ɗan tauri a ƙauyen Dogon-Daji da ke Ƙaramar Hukumar Garko a Jihar Kaduna.

Wani shugaban al’ummar yankin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun  fille kan ɗan taurin mai suna Garba Sarki ne bayan sun jima suna bibiyarsa.

Ya ci gaba da cewa ’yan bindigar sun ƙullaci Garba Sarki ne tun bayan wani artabu da ya yi da su a daji inda ya kashe biyu daga cikinsu a watannin baya.

A cewarsa, daga bisani suka sake yin karon batta, inda ’yan bindigar suka buɗe wa ɗan taurin wuta amma ba ta kama shi ba.

Ganin haka ne suka yi taron dangi suka kama shi da ƙarfin tsiya suka ɗaure, suka yi masa yankan rago.

Ya ƙara da cewa an yi wa Garba Sarki wannan kisan gilla ne a cikin daren Alhamis a cikin dokar daji.

Shugaban al’ummar ya ce sai ranar Asabar aka gano gawar mamacin inda aka tura ’yan banga suka ɗauko ta aka sallace ta.

Wani ɗan banga a yankin mai suna Haruna ya ce, mamacin “ya dade yana ragargazar ’yan bindiga a yakin, a kwanakin baya ma ya kashe ’yan bindiga biyu.”

Ƙoƙarin wakilinmu na samun ƙarin haske kan wannan lamari daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna,  ASP Hassan Mansur bai yi nasara ba.

Jami’in hulɗa da jama’an bai amsa kiran da aka yi masa ba har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan labari.

By ukarofi