
Daga KHALIFA MUHAMMAD
Wata babbar mota ɗauke da kaya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 biyo bayan ƙwacewa da ta yi a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura, a Jihar Kano.
Haɗarin, ya faru ne a ranar juma’a yayinda wasu masallata ke kan hanyar komawa gida bayan gabatar da sallar juma’a inda nan take ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha huɗu tare da raunata wasu da dama.
A lokacin da yake jawabi, Kwamandan reshen jihar Kano na hukumar kula da haɗurra ta ƙasa (FRSC), Ibrahim Abdullahi, ya ce sun tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 1:50 na rana da wata mota mai ɗauke lamba kamar haka; MKA 537 XN.
Abdullahi ya ce, jin labarin ke da wuya, hukumarsu ta tura wasu jami’anta zuwa wajen da abin ya faru domin tabbatarwa da kuma ba da kula ga waɗanda suka raunata sakamakon haɗarin.
Ya kuma miƙa gaisuwar ta’aziyyarsu ga waɗanda lamarin ya shafa tare da kira ga al’umma da su riƙa kiyaye bin umarnin alamomin kan hanya don kaucewa faruwar irin haka a gaba.
