
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ɗan wasan Nijeriya da ke buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atalanta, Ademola Lookman ya lashe kyautar ɗan wasan gwarzon shekara na kakar wasan 2023/2024 a ƙungiyar biyo baya taka rawar gani da ya yi.
Lookman mai shekaru 26, ya yi ƙoƙari wajen nuna bajinta wa ƙungiyar a gasar ‘Serie A’ ta ƙasar Italiya wanda hakan ta sa ya kai Atalanta ga nasarar lashe kofin gasar ‘Europa’ inda ya zura ƙwallaye uku a wasan ƙarshe tsakanin kulob ɗinsa da ƙungiyar Bayer Leverkusen ta ƙasar Jamus.
Har ila yau, Lookman ya lashe kyautar cin ƙwallo mafi kyau a gasar Europa, sannan kuma ya ci jimillar ƙwallaye 11 tare da bada 8 da aka ci a cikin wasanni 31 da ya buga wa Atalanta a kakar.
