
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rahotanni daga Jihar Katsina sun ce Rundunar ‘Yan sandan jihar ta kama mutum biyu da ake zargin su da hannu a garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Dauda Ƙahutu Rarara, Hajiya Ibrahim.
Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce ana cigaba da binciken waɗanda aka kama, a ƙoƙarinsu na ceto ta.
A yau juma’a ne aka yi garkuwa da Hajiyar mai kimanin shekaru 75 a ƙauyen Kahutu dake Ƙaramar Hukumar Danja, a Jihar Kastina da misalin ƙarfe 1:30 na rana.
Wannan wani huɓɓasa ne da rundunar ‘Yan sandan ta yi wajen ganin an daƙile ayyukan garkuwa da mutane da makamantansu a yankin.
