27
Jun
Daga KHADIJA ABUBAKAR Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da shirin gina ƙasa da tallafawa magidanta a yayin wani zama da Majilisar kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa, NEC a Abuja. Wani jawabi da ya fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya ce manufar shirin su ne dan a inganta harkokin noma da tattalin arziƙi gami da bada tallafi domin rage raɗaɗin talauci ga ƴan Najeriya. Shirin wanda ya samu goyon bayan Majalisar ta NEC, ya ƙunshi rarraba kuɗaɗe da yin ayyukan more rayuwa a dukkan shiyyoyin ƙasarnan guda shida, inda za a bada tallafin Naira…
