Babaji

5434 Posts

Gwamnan Sakkwato ya musanta shirin tuɓe Sarkin Musulmi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu ya musanta zargin da ƙungiyar ƴancin musulmin Najeriya (MURIC), ta yi na cewa yana shirin tuɓe Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III daga kujerarsa. A kwanakin baya ne babban daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya tada batun, inda ya ce gwamnati Jihar na shirin korar Sultan Sa'ad Abubakar daga muƙaminsa la'akari da rikicin Masarauta da ke cigaba da aukuwa a Jihar Kano. Farfesan ya yi gargaɗin cewa, al'ummar musulmi a Najeriya ba za su amince da hukuncin sauke Sarkin ba inda ya ce Sarki Sa'ad ba Sarkin gargajiya ba…
Read More

A guji amfani da maganin ‘B-GAG’ – Hukumar NAFDAC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da dokar abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta yi kira ga ƴan Najeriya da su guji saya ko amfani da wani magani mai suna 'B-GAG' na ruwa, sakamakon shiga kasuwa da ya yi ba tare da cike ƙa'idoji ko yin rijista da hukumar ba. Bayanin ya fito ne daga ofishin darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye a wata takardar sanarwa mai lamba 023/2024 a ranar Lahadin da ta gabata inda ta ce, ana sayar maganin wanda ba a tantance ko yi masa rijista ba daga wani kamfani mai suna 'Babban Gida Agalawa…
Read More

Iyalan ɗalibin sekandiren NAF da aka kashe sun buƙaci a yi adalci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Iyalai da wakilan cocin wani mataimakin shugaban daliban makarantar sekandire ta rundunar sojin sama (NAF) da ke Kaduna, Felix Blaise da aka kashe, sun buƙaci hukuma da ta yi adalci yayin binciken kisan Ɗalibin mai shekaru 15, ɗan aji biyar, ana zargin an kashe shi ne a ɗakin kwanan ɗalibai inda wata jarida ta yanar gizo ta ce wasu ɗalibai su biyu ƴan aji shida ne suka sa masa lantarki wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. NAF ta ce, tana cigaba da bincike kan lamarin domin gano haƙikanin abun da ya faru. Haka nan, wakilin cocin…
Read More

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a kisan wani babban soja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar Ƴan sanda ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi kan kisan tsohon shugaban rundunar soji na ƙasa kuma jami'i Mai ritaya, Burgediya Janar, Harold Udokwere. Jaridar 'Blueprint' ta ruwaito cewa an kashe babban sojan ne a gidansa dake layin Sanga, a rukunin gidajen Sunshine, a unguwar Lokogoma dake Abuja a yayin wani fashi da wasu ƴan bindiga suka kai yankin. An samu bayanin ne a wani faifan bidiyo da ke ɗauke da rubutu inda waɗanda aka kama sun haɗa da; Ibrahim Rabi'u, mai shekaru 33 daga Ƙaramar Hukumar Dala, Jihar Kano mazaunin Rasha Apo…
Read More

Rikicin Masarauta-Rundunar Ƴan sandan Kano ta kori masu gadi a fadojin da Sunusi da Aminu suke tare da ƙara jami’ai

Daga Farouk Abbas Rundunar Ƴan sandan Jihar Kano ta aika da ƙarin jami'anta zuwa fadojin da Sarki Sunusi Lamido Sunusi da kuma Sarki Aminu Ado Bayero su ke, biyo bayan ɗar-ɗar na faruwar rikici a yankunan Masarautun. Tuni dai mafarauta da sauran masu gadin Masarautun suka bar fadojin a lokacin da jami'an suka isa, don inganta tsaro ga rayuka da dokiyoyin al'ummar yankunan. Kwamishinan Ƴan sandan Jihar, Usiani Gumel ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai inda ya ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da wadataccen tsaro a faɗin Jihar. Usaini Gumel ya ce "an tura jami'ai…
Read More

An gano kadarorin naira tiriliyan 1.49 a Dubai, mallakar ƴan Najeriya ciki har da El-Rufa’i da ƴar Atiku da Baba Ahmad da sauransu

Daga Edita Cikin shekaru huɗu, adadin ƴan siyasar da asirin su ya tuno a Najeriya (PEPs), ya ninka inda a shekarar 2020, bincike ya nuna cewa gidaje 800 da ƙudinsu ya kai dala miliyan 400 a Dubai da ke ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa mallakan ƴan Najeriya ne wanda kuma a shekarar 2024 sun kai kimanin mutum 1,600 wanda kuɗin su ya kai kusan dala biliyan 1. Tawagar aikin bincike kan rahoton laifukan sata da almundahana da dukiyar al'umma (OCCRP), ita ce ta gudanar da binciken tare da gidajen jaridu guda 70 yayin da Jaridar 'Economy Post' ta wakilci Najeriya. Rahoton…
Read More

Sirikar Ganduje ta rasu

Daga Maimuna Bashir Isa Sirikar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Hajiya Asiya Muhammad Gauyama ta rasu. Mai taimaka wa Ganduje kan harkokin yaɗa labarai, Edwin Olofu ya yi jawabin cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce, marigayiyar ta kasance mahaifiya ga matar Ganduje, Farfesa Hafsatu Abdullahi Umar Ganduje wacce ta rasu da asubahin ranar Litinin. Za a yi jana'izar ta a yau da misalin ƙarfe 2 na rana a gidan Ganduje da ke kan hanyar Miyangu a Jihar Kano. Ya kuma ce wannan babban rashi ne ga iyalanta da ma duk mutanen da suka…
Read More

Shettima da Idris za su halarci ƙaddamar da littafin babban editan ‘Leadership’ a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai girma mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima zai zama babban baƙo a taron ƙaddamar da littafin 'Writing for Media and Monetising It', wanda babban editan jaridar 'Leadership', Azu Ishiekwene ya wallafa kuma maɗaba'ar buga littafai ta 'premium times' ta buga, don samun lada ga rubutattun abubuwa masu kima. Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Alhaji Idris Muhammed shi zai jagoranci ƙaddamar da littafin wanda za a yi a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, 2024 da misalin ƙarfe 10 na safe a ɗakin taro na Yar'adua Centre da ke Abuja. Mawallafin tare da maɗaba'ar sun…
Read More

Ministan yaɗa labarai zai jagoranci buɗe taron tallace-tallace na 2024 a Legas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Za'a gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, inda manyan mahlarta taron suka haɗa da ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Muhammed wanda shi ne shugaban taron da shugaban hukumar hana fatauci da miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Janar Buba Marwa Mai ritaya da wanda ya ƙirƙiri cibiyar kimiyyar 'Data' ta ƙasa, Dakta Bayo Adekanbi da kuma babban sakataren ofishin kula da kuɗaɗen makarantun gaba da sekadire, 'ARC.' Sonny Echono da sauran su. Hukumar kula da harkokin tallace-tallace ta ƙasa (ARCON) ta shirya taron inda shugaban NDLEA, Buba Marwa zai…
Read More

“Kar ka sauke Sarkin Musulmi”- MURIC ta gargaɗi Gwamnan Sakkwato

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar kare ƴancin al'ummar musulmin Najeriya (MURIC), ta gargaɗi gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Ahmad cewa kar ya sauke Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar, daga kan muƙaminsa. MURIC ta yi wannan gargaɗi ne biyo bayan da gwamnan ya sauke sarakunan gargajiya guda 15 a faɗin Jihar watanni biyu da suka wuce inda jita-jitar sauke Sarkin Musulmin ke yawo wanda hakan ya sa ƙungiyar ta nuna damuwa tare da kira ga gwamnan da ya guji duk wani yunƙuri na sauke Sarkin Musulmi daga kujerarsa. Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar…
Read More