24
Jun
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata tawagar al'ummar Jihar Kano ta yi kira ga gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf da ya sauka daga kan kujerar shugabancin Jihar domin martaba doka da oda. Wani mamban tawagar mai suna Muhammad Bello ya faɗi hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun yi kiran ga gwamnan ne sakamakon ƙin biyayya ga hukuncin da kotu ta yi na rushe cancantar zaman Sunusi Lamido Sunusi a matsayin halstaccen Sarki. Bello ya ƙara da cewa, ƙin amincewa da hukuncin Alƙali Abdullahi Liman a babbar kotun tarayya ga gwamnan, alama ce dake nuna cewa yana rashin ladabi ga…
