Rikicin Masarauta: Aminu Ado ya ɗaga tuta a fadar Nasarawa

Spread the love

Daga Sadiq

Yayin da ake tsaka da rikicin masarautar Kano, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya ɗaga tutar mulki a ƙaramar fadar da ke Nassarawa inda hakan ke nuna iko da Sarkin yake da shi a yanzu.

A bisa al’ada, tutar na zama ne a matsayin alamar iko, kuma ɗaga ta na alamta cewa sarki yana cikin fada.

Hakan kuwa na zuwa ne duk da umarnin gwamnatin Kano ga Sarki Aminu na ya fice daga fadar a yayin da ake cigaba da dambarwar sarautar Kano.

Akan ɗaga tutar ce da misalin karfe 6 na safe a kuma sauke ta 6 na yamma ko idan sarki ya yi bulaguron aiki.

Kano ta shiga rikicin masarauta tun bayan da gwamnatin jihar ta rushe masarautun Bichi, Karaye, Rano da Gaya wanda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙiro.

Rikicin na cigaba da haifar da ruɗani yayin da Aminu Ado da Sarkin Kano na 14, Muhammdu Sanusi II kowa ke cigaba da ikirarin shi ne Sarkin Kano.

By Babaji