Rikicin masarauta: Na zo Kano don aiki, ba don wasu ba – Kwamishinan ‘Yan Sanda

Sabon Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Salman Dogo ya musanta zargin da ake na cewa yana da alaƙa da Sarkin Kano da aka tuɓe, Aminu Ado Bayero.

Yace yazo Kano ne domin ya hidimtawa al’umma baki ɗaya. Ba batun bambancin addini ko ƙabila. Domin yace shi ɗan Najeriya ne, don haka aikinsa shine ya hidimtawa Najeriya ko a ina.

Ya roƙi cewa yan Kano su bashi haɗin kai domin ganin sun yi maganin abunda ke damun jihar.