Daga Umar Akilu Majeri Dutse
Wata Guguwa Mai ƙarfin gaske da ruwan Sama mai ƙarfin gaske sunyi sanadin ruguza Gine Gine masu yawa a makarantar nazarin Kiwon Lafiya ta Jahun a daidai lokacin da ɗalibai suke ƙoƙarin dawowa makarantar domin cigaban da zangon karatu karon farko.
Guguwar tayi Mummunan ta adi wadda idan gwamnatin batayi wani na mijin ƙoƙari za aiya samun tangarɗa a harkokin karatu na makarantar dubada yadda gwamnatin ta damu akan Matsalar karancin likitoci da karancin ma aikatan lafiya a fadin asibitocin dake jihar da Kuma yadda Gwamnatin tàke kashe makudan kudade a duk shekara da nufin Magance matsalar karancin ma aikatan lafiya a fadin jihar.
Jawabin hakan ya fitone daga bakin wani Mutun Maison cigaban Jihar jigawa Kuma mazaunin makarantar daya Sanar da wakilimmu halin da makarantar tàke ciki Kuma ya bukaci a sakaya sunansa yace guguwar da Ruwan sama sun lalata mahimman wurare masu yawa ciki harda dakin daukar darasin dalibai wato student complex building wadda aƙalla yana daukar dalibai Kamar dubu uku 3000 a lokacin daya.
Yace iskar ta yaye wani sashi na ginegine. Kuma ya zubo da silin na wasu ajujuwan da manyan ofisoshi da Kuma ɗakunan binciken kimiyya wadda gyaransu yana bukatar miliyoyin naira inji Mai korafin.
Kamar yadda binciken yanuna haka zalika gidan inji dayake baiwa makarantar hasken wutar lantarki da ruwansha shima rufinsa ya afka yayinda fanel fanel na Sola dake saman gidan injin Iska ta tarwatsasu lamarin dayasa aka Sami tsaiko na hasken wutar lantarki a wasu sassa na makarantar Kuma aka sami matsalar ƙarancin ruwansha a makarantar baki daya saboda matsalar tashin wutar.
Hakan yasa hukumar makarantar ta sayo sabbin allunan sola ,sola ta hadawa rijiyoyin samarda ruwan Sha na makarantar saboda a magance matsalar rashin ruwan da kuma samarda hasken wuta saboda dawowar dalibai makarantar kasancewar hutunsu ya Kare za a shiga sabon seshin nazarin karatu
.Sauran wuraren da ta adin iskar ya shafa sun hada da zauran gani da ido na ɓangaren lura da tsaftar mahalli wato environmental demonstration ground da Kuma wasu ajunuwan da sanata Babangida ya Gina ƙarƙashin MDGs projects Shima Yana daga Cikin waɗanda iskar ta lalata rufinsu gaba daya wadda ananne masu nazarin karatun hakori suke ɗaukar darasi wato dental course.
Binciken da aka gudanar ya nuna hatta ɗakin inji da yake samarda hasken wutar lantarki a makarantar ya rufta babu damar ayi anfani da injin Makarantar wadda hakan yayi sanadin tarwatsewar dukkanin fanel fanel da aka ɗora bisa rufin kwanon gidan injin wadda ake anfani dashi wajan samarda hasken wutar lantarki da Samar da ruwansha a faɗin makarantar , sakamakon haka ya tarwatse aka rasa wuta lamarin daya jefa wasu sassa na makarantar chikin wani yanayi na rashin wuta musamman ofishin malamai da na shugaban makarantar da dakunan gwaje gwaje na kimiyya dake makarantar.
Amma Kamar yadda binciken ya nuna babu wurin dayafi samun ɓarna babu Kamar ajunuwan dalibai da ake cewa students complex room wadda yake iya daukar ɗalibai samada mutun 3000 a sahin Shiya koyan karatu wato lecture rooms. Yaƙara da cewar akwai bukatar a gyara shi da wuri kasancewar dalibai sun Fara dawowa domin cigaba da zangon karatu na farko a makarantar wato first semester.
Saboda haka an buƙaci gwamnatin jihar jigawa ta kawowa makarantar agajin gaggawa da nufin kaucewa dukkan Wata matsala da ɗaliban zasu iya fuskanta a wanna zangon karatun Kamar yadda yake korafi yace matuƙar gwamnatin bata baiwa lamarin kulawar data dace ba ta gaggawa za a iya samun katuwar matsala a makarantar domin a ruwan da akayi na daren lahadin data gabata Saida Iska ta sake yaye wani sashi na ɗakunan kwanan dalibai maza lamarin dayasa kayan dalibai masu yawa suka lalace kasancewar ɗaliban suna hutu basa makarantar alokacin da iskar tayi ɓarnar .
Yakuma koka akan yanayin bandakunan wankan ɗaliban dakuma banɗakunan bahaya musamman banɗakunan ɗalibai Mata da suka jima alalace haka sukansu na dalibai maza Suma a lalace suke,takai ta kawo mutun bazai iya hadiyar Koda yawu ba saboda kazantar dake cikinsu.Lamarin dayasa dalibai da dama yin bahaya a wajen harabar dakunan kwanansu saboda gudun kada su dauki wata cuta a jikinsu a matsayinsu na daliban Kiwon Lafiya .
Binciken da wakilimmu yayi ya gano sauran ɗakunan da iskar ta lalata sun hada harda physic laboratory ,biology laboratory da chemistry lab wurin da dalibai suke aiwatar da gwaje gwaje duk iskar ta yayesu saboda gara ta cinye katakayen ta lalata silin ɗin shiyasa iskar ta Sami damar lalata Gine ginen Sauran wuraren da abin ya shafa sun hada da ginin BME studio da ofishin HOD Dental ,HOD Medical lab ofishin Director medical lab ,bio medical, Enginearing workshop ,bio medical lab ,da demonstration rooms da akeyiwa dalibai gwajin makamar aikin duk iskar ta wargazasu.
Kamar yadda bayanai suka nuna hatta ofishin shugaban Makarantar gara tayimar kacha kacha lamarin dayasa iskar ta Sami nasara wajan yaye rufin ofishin Kuma silin da akasa a ofishin dayake ya tarwatse ya afka Cikin ofishin lamarin daya tashi hankalin kowa a makarantar akayiwa aikin shigar hanzari aka gyara wasu wuraren domin hana iskar cigabada lalata gine ginen makarantar.
Hakan yasa wakilimmu ya garzaya Makarantar domin jinta bakin shugaban Makarantar akan Gaskiyar labarin domin tabbatar da sahihanchin labarin dayake amsa tanbayoyin manema labarai shugaban makarantar Malam Abdullahi Abubakar ya tabbatar cewar Iska tayi masu barna a makarantar amma tuni suka gyara a wasu wuraren da iskar tayi masu barnar yakuma Kara da cewar sauran manyan wuraren da bazasu iya gyarawa ba sun sanar da gwamnatin jihar halinda suke ciki domin a gyara masu bayan sun dauki hotunan wuraren da suka lalace sun tura.
Yaƙara da cewar hukumar Makarantar ta kashe kimanin naira miliyan biyu wajan gyaran dakunan kwanan dalibai mata da maza da ofishin shugaban makarantar wato provost da wasu ajunuwan da iskar bata lalata sosaiba Yaƙara da cewar wuraren da iskar tafi barna sun hada ICT Library da class room complex da dakin inji da wurin gwaje gwaje wato demonstration room na environment da Ajunuwan MDGs wadda akwai buƙatar agajin gaggawa domin Ganin angyarasu kafin dalibai su kammala dawowa makarantar.
Daya juya batun ruwansha amakarantar yace sunyi kokarin sun sayi sabbin fanel fanel sun sake kafawa Kuma sun hadasu da rijiyoyinsu Ana samun ruwa da hasken wutar lantarki saboda gudun kada dalibai da malaman makarantar su fada Wani irin yanayi na damuwa domin ruwa shine rabin rayuwar ɗan Adam .
Saboda hakanema ya buƙaci gwamnatin jihar data kawo was makarantar agajin gaggawa ta hanyar Samar masu da Karin fitulu masu aiki da hasken Rana da Kuma Karin fanel fanel da injin SoMo domin a karawa riniyoyin karfin wuta ta yadda za a Sami wadataccen ruwansha a makarantar tareda samun hasken wutar lantarki yadda tsarin zai Kara inganta a makarantar Yaci gabada cewa zasu ɗauki matakin kariya a makarantar ta hanyar dasa bishiyoyi da zasu zagaye harabar makarantar domin Hana iskar cigaba Yi masu barna a makarantar saboda haka zai dasa irin darbejiya dubu uku a gefen katangar da za a zagaye makarantar saboda ya lura karancin bishiyoyi Yana taimakawa wajan haifarda barazanar Iska datake lalata masu gine Gine a duk shekara.A wajan bangaren karancin banɗakunan makarantar Kuma ya buƙaci gwamnatin ta samarda Karin bandakuna domin anfanin dalibai maza da dalibai Mata saboda karancin bandakunanne yasa ake samun matsalar kazanta Kuma magana ta gaskiya bandakunan sun lalace ne saboda dadewarsu tsawon shekaru ana anfani dasu tunda aka Gina makarantar samada shekaru 35 Dan haka akwai bukar Ace an Samar da ƙarin banɗakunan a makarantar injishi .