Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kungiyar ƴan kishin Kano tsantsa wato Kano Patriotic Front (KPF) ta bayyana matukar kaɗuwar ta tare da yin Allah-wadai da yadda matsalar tsaro ta sake kunno kai a jihar Kano, musamman hare-haren Ƴandaba da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Manjo Janar Ibrahim Sani (mai ritaya)da mataimakinsa Alh. Ahmed Shehu Yakasai, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen ganin an kawo ƙarshen hare-haren da ake kaiwa ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.Dakarun kishin Kano sun kuma yi kira ga iyaye da dattawan al’umma da sauran jama’a da su haɗa kai da gwamnati da jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.
Sun jaddada mahimmancin iyaye su ɗauki cikakken alhakin kula da tarbiyyar ‘ya’yansu domin rage yawan aikata laifukan yara.Kazalika ƙungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro da su gano tare da kamo ‘yan ta’adda a cikin al’umma tare da tabbatar da sun fuskanci hukuncin ayyukan da suka aikata.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a baya-bayan nan ya sabawa ka’ida da kimar al’ummar Kano, kuma ƙungiyar ta himmatu wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
