Shugaba Tinubu ya yi wa Sanata Ali Modu Sheriff ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Daga Abdullahi Maitama Sani

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika saƙon ta’aziyyarsa ga tsohon gwamnan Jihar Barno, Sanata Ali Modu Sheriff kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Aisha.

Za a gudanar da jana’izar Hajiya Aisha da ta rasu da shekaru 93 a gidansu na marigayi Galadima Modu Sheriff da ke kan hanyar Damboa a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno.

Wata sanarwa da ta fito daga mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ta ce shugaba Tinubu na jajenta wa iyalan Sanatan kan babban rashin da aka yi mu su, yana mai rarrashin su tare da addu’ar fatan samun rahamar Allah ga marigayiyar inji sanarwar.