
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ce Naira dubu ɗari huɗu a ke biyan sa duk wata a lokacin da ya ke shugabantar majalisar, saɓanin yadda a ke ta yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa maƙudan kuɗaɗe ƴan majalisu ke ɗauka a matsayin albashi.
Dogara, wanda shi ne Kakakin a majalisa ta takwas (daga 2015, zuwa 2019), ya faɗi haka ne a zauren Majalisar da ke Abuja yayin jawabin fatan alkhairi ga ƴan majalisu a bikin satin majalisar ƙasa.
Ya ce, kuɗin albashi da alawus ɗin da ya ke karɓa sun kai jimillar Naira miliyan 25 waɗanda ya ce ba sa isan buƙatu da dama da a ke da su a mazaɓarsa.
Sannan, ya ce bai taɓa kashe wani ɓangare na alawus ɗin da ya ke karɓa ba, hasali ma ya sa an buɗe wani asusun banki na musamman ne domin yin ayyukan buƙatun ƴan mazaɓar tasa da ta sauran ƴan ƙasa a tsawon shekaru huɗun da ya yi a kujerar.
Ya ƙara da cewa, kuɗin bai wuce kwana uku saboda yawaitar neman taimako daga mutane musamman ƴan yankin sa.
Kazalika, kuma ya yi kira ga al’umma da ta bai wa demokradiyya haɗin kai ganin yadda ta ke da daraja, domin ita ce tsarin da ke bada dama ga kowane ɓangare shiga harkar siyasa.