Babaji

5681 Posts

Za a fara cirar kuɗi da katin ɗan ƙasa a watan Agusta-NIMC

Daga Khadija Abubakar Hukumar kula da katin zama ɗan ƙasa (NIMC), ta ce nan da watanni biyu za ta inganta katin zama ɗan ƙasa ta yadda zai ke amfani guda uku ga masu shi. Wani jami'in hukumar da bai yadda a faɗi sunansa ba ya sanar manema labarai hakan a ranar Juma'a, inda ya ce kati zai fara amfani a matsayin shedar zama ɗan ƙasa, da ɓangaren cirar kuɗi kamar katin 'ATM' sannan da kuma wasu harkokin rayuwa. Ya ƙara da cewa, hukumar tana iya ƙoƙarinta wajen cimma hakan, domin kuwa a halin yanzu, ta fara gwajin yiwuwar haka, dan…
Read More

Kotu ta bada umurnin riƙo na din-din-din ga kadarorin naira biliyan 12 da ke da alaƙa da Emefiele

Daga Sadiq Muhammad Wata babbar kotun tarayya dake Jihar Legas, ta jaddada cewa, za a cigaba da riƙe kadarorin gwamnatin tarayya da aka ƙwace a hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele waɗanda adadinsu ya kai sama da naira biliyan goma sha biyu. Mai Shari'a Chukwujekwu Aneke, ya yi hukuncin biyo bayan da wani jami'in hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da laifukan da suka shafi kuɗi (EFCC), Chineye Okezie ya shigar da ƙara, inda ya ce a shari'ar karo na ƙarshe, za cigaba da riƙe kadarorin na din-din-din. A ranar 5 ga watan Yuni, 2024…
Read More

Rundunar Soji ta hallaka ƙasurgumin ɗan ta’adda a Kaduna

Daga Bala Muhammad Rundunar Sojin Najeriya, ta ce ta kashe wani sanannen ɗan ta'adda mai suna Kachalla Ragas tare da wasu gungun ƴan ta'adda a wani hari da ta kai a ƙaramar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna. Kwamishinan sa-ido kan aikin jami'an na ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar da sanarwar, inda ya ce jami'an sun kai harin ne ƙarƙashin atsayen 'Whiri Punch' wanda ya yi sanadiyar mutuwar ƴan bindigan da dama ciki har da manyan kwamandojinsu a yankin ƙauyen Bula dake dajin Yadi a ƙaramar hukumar. Yayin miƙa rahoton ga gwamnatin Jihar, Samuel ya ce…
Read More

Ƴar Galadiman Dutse mai shekaru 62 ta rasu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Iyalan gidan Galadiman Dutse, Alhaji Basiru Muhammad Sanunsi na cikin alhini, biyo bayan rasuwar ɗaya daga cikin ƴaƴansu mai suna Hafsatu Basiru Sanusi. Marigayiyar wacce aka haifa a ranar 31 ga watan Mayu, 1962, ta bar ƴaƴa huɗu cikin har da Lukman Mahmoud Isa Dutse, ma'aikacin bankin CBN reshen Abuja, da kuma Alawiyyah Mahmoud Isa Dutse, ma'aikaciyar kamfanin inshora na ƙasa (NDIC) dake Abuja. Wasu daga cikin ƴan uwanta sun haɗa da; Jamilu Basiru Sanusi, Turakin Dutse da Zahraddeen Basiru Sanusi, Dan Isan Dutse, da kuma Sanusi Basiru Sanusi, Ɗan Darman Dutse. Hafsatu ta kasance jigo…
Read More

Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ware naira biliyan 21 domin bai wa ƴan Najeriya mitocin lantarki kyauta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta sanar da ware kimanin naira biliyan ashirin da ɗaya ga kamfanonin wutar lantarki guda 11, domin bai wa ƴan Najeriya masu amfani da lantarki mitoci a kyauta. Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa (NERC), ta faɗi hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 21 ga watan Yuni, 2024. Sanarwar ta ce, za'a raba mitocin ne ga waɗanda basu da shi a gidajensu ko wuraren sana'o'insu a ƴan watanni kaɗan masu zuwa. Hukumar ta ƙara da cewa, wannan huɓɓasa da gwamnatin ta yi, zai taimaka wajen haɓaka asusun kamfanonin ta…
Read More

CAF ta sanar da lokacin gasar AFCON na 2025

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, (CAF) ta ce za'a gudanar da gasar cin kofin Nahiyar Afirka, (AFCON) a tsakanin 21 ga watan Disamba, 2025 da kuma 18 ga watan Janairun 2026 wanda za'a yi a ƙasar, Moroko dake Arewacin Afirka. CAF ta yanke hakan ne, a yayin wani zaman manyan ofisoshinta da ta saba yi, a ranar juma'a inda ta ce da ta so gudanar da gasar a lokacin bazara ne a cikin shekarar 2025, amma saboda ya haɗu lokacin gasar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta duniya, sai ta mayar da shi zuwa ƙarshen shekarar. Za'a gudanar…
Read More

Trump ya yi alƙawarin katin ɗan ƙasa ga ƴan ƙasar waje da suka yi difuloma a Amurka

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan takarar jam'iyyar 'Republican' kuma tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya yi alƙawarin mallaka wa dukkan ƴan ƙasar waje katin zama ɗan ƙasa matukar mutum ya yi karatun matakin difuloma a ƙasar. Trump, ya faɗi hakan ne a wata hira da ƴan jaridu, jim kaɗan bayan babban abokin hamayyarsa kuma shugaban ƙasar na yanzu, Joe Biden ya shelanta cewa za'a ƙwace matsayin ƴancin zama ɗan ƙasa ga duk waɗanda suka auri ƴan Amurka da ba ƴan ƙasa ba a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen magance matsalar zama ɗan ƙasa ba bisa ƙa'ida ba da wasu da…
Read More

Za a kammala aikin filin jirgin saman Gusau cikin wata uku-Gwamnan Zamfara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce za a kammala aikin filin jirgin saman Gusau cikin nan da wata uku. Gwamnan ya faɗi hakan ne a yayin taron buɗe aikin filin jirgin wanda Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya yi a Gusau, babban birnin Jihar a ranar Alhamis da ta gabata. A wani jawabi daga mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Idris, an ƙaddamar da aikin filin jirgin ne domin yin sufuri a cikin gida Najeriya da kuma ƙasashen waje. Ya ƙara da cewa, aikin zai ci tsawon kilomita 3 zuwa 4…
Read More

Aikin tashar ‘gas’ na AKK zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin Arewacin Najeriya – Ministan Labarai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Mohammed Idris ya ce aikin tashar iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano, zai taimaka wajen inganta tattalin arziƙin Arewacin Najeriya. Ministan ya faɗi haka ne ta ofishin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim a yayin wani ziyaran gani da ido da ya kai wajen aikin a Jihar Kaduna tare da Ministocin kuɗi da tattali, Wale Edun da ƙaramin ministan albarkatun iskar gas, Ekperikpe Ekpo da kuma shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari. Ya kuma ce, aikin zai sa a samu yawaitar amfani da iskar gas a gidaje da wajen…
Read More

Gwamnatin Tinubu za ta sayo wa Fadar Shugaban Ƙasa sabon jirgi bayan gwanjon tsofaffin jirage uku

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar sayar da tsofaffin jiragen sama na ofishin shugaban ƙasa domin sayo sabo wa ofishin. Hakan ya faru ne bayan da kwamitin majalisar wakilai kan tsaron ƙasa da basira ya bada shawarar cewa akwai buƙatar a sayo jirage guda biyu domin amfanin shugaban ƙasa da na mataimakinsa. Shugaban kwamitin na ɓangaren majalisar dattijai, Shehu Buba Umar ya bada goyon bayansa kan shawarar majalisar wakilan. Rahoton ya ƙara da cewa, sayar da jiragen zai taimaka wajen samun daidaito kan adadin da ake buƙata a ofishin, domin yanzu haka akwai jirage gama gari guda…
Read More