Babaji

5684 Posts

Henna Ball da People’s Award na 2026: Gidan talabijin na Tozali zai yi taron dawo da karsashin matan da aka yi garkuwa da su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gidan talabijin na Tozali na farin cikin sanar da al'umma cewa zai gudanar da taron bayar da lambar yabo na Henna Ball da Tozali People na 2026. Za a gudanar da taron ne a ranar 31 ga watan Oktoba, 2026 a ɗakin taro na Los Angeles, inda za a martaba ƙoƙari, al'ada, jajircewa da tasirin ayyukan jin-ƙai acikin al'umma. Haka kuma, an yi wa taron laƙabi da Empowering Survivors. Restoring Hope.", wato mai manufar inganta rayuwar matan da suka shaƙi iskar 'yanci bayan garkuwa da su da kuma dawo da karsashinsu acikin al'umma. Sannan,…
Read More

Mutane 13 sun rasu, ana riƙe da yara 12 har yanzu – Ba’asin ‘yan Kwara da suka shaƙi iskar ‘yanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu daga cikin mutanen ƙauyukan Woro da Nuku na Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara da suka shaƙi iskar 'yanci bayan harin ranar 3 ga Fabrairu, sun bayyana cewa mutane 13 sun rasu a lokacin da suke hannun 'yan bindiga, yayin da kuma har yanzu akwai yara guda 12 da ke komar 'yan ta'adda. Sun bayyana haka ne ga manema labarai bayan Gwamnatin Jihar Kwara ta karɓi baƙuncinsu a hukumance, inda suka bayyana yadda suka tsinci kansu a daji da rayuwar cin abinci sau guda a yini na tsawon kusan watanni shida. Mutanen na…
Read More

Mourinho ya sanya dokoki huɗu don dawo da ɗa’a a Real Madrid

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sabon kociyan Real Madrid ta Ƙasar Sifaniya, Jose Mourinho, ya samar da wasu dokoki guda huɗu da nufin dawo da ɗa'a, ƙwarewa da haɗin kai acikin 'yan wasan ƙungiyar. A cewar jaridar Sifaniya AS, ɗan ƙasar Portugal ɗin mai shekaru 63 ya gano wasu ɗabi'u da yake ganin akwai buƙatar a sauya su tun bayan dawowarsa Bernabeu. Kocin ya samar da sababbin tsarin gudanarwa akan cin abinci, tsare aiki, gyaran tsarin kula da lamuran raunin 'yan wasa sa kuma dunƙule tawagar 'yan wasa. A sabon wa'adin nasa, 'yan wasan Real Madrid za su kasance…
Read More

Jagoran Tijjaniya ya nemi ƙarfafa alaƙar Nijeriya da Aljeriya bayan ganawa da Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kalifan Ɗarikar Tijjaniyya kuma Jagoran Majalisar Ƙolinta, Sheikh Sidi Ali Belarabi Tidjani, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja a matsayin wani bangarena ziyararsa ta zuwa Nijeriya a hukumance. Sheikh Tidjani ya isa Nijeriya ne a ranar Alhamis tare da wata tawaga daga Zawiyar Kalifanci da ke Aïn Madhi a Aljeriya, bayan wata gayyata ta musamman daga jagororin Tijjaniyya a Nijeriya. A yayin haka ne ya yi tsokaci kan daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Aljeriya, tare da nuna kwaɗayin ƙarfafa alaƙar ta hanyoyi da dama da suka shafi ci-gaba. Tawagar…
Read More

Matakin EFCC na rufe asusun gwamnatin Osun na bisa doka, inji Falana

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Lauyan kare haƙƙin ɗan-adam kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Femi Falana, ya kare matakin Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, inda ya ce ta yi aiki ne bisa ikon da doka ta ba ta a lokacin da ta sanya wa asusun gwamnatin Jihar Osun takunkumi. Falana ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a a shirin 'Politics Today', a inda ya ce hukumar ba ta yi wani abu da ya saɓa wa doka ba, kuma Shugaba Bola Tinubu ma yana sane da halascin matakin…
Read More

An karrama gwamnan Zamfara da lambar yabo ta ZIK Pan-African a Ghana

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu babbar kyauta ta lambar yabo ta 'ZIK International Peace and Leadership Award' da aka gudanar a ƙasar Ghana bisa la’akari da nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata. An gudanar da bikin bayar da lambar yabon karo na bakwai ne a ranar Juma’a a cibiyar British Council da ke Accra, babban birnin ƙasar. A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce an yi wa taron take da “Jagoranci, Zaman Lafiya da Haɗin Kan Yankuna: Bunƙasa Ci gaban Afirka…
Read More

Gwamnatin Kano ta goyi bayan Gwamnatin Tarayya kan hana wasu mallakar rukunin cibiyar kula da gandun daji

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnatin Tarayya wajen kare wani ɓangare na Sashen Cibiyar kula da Harkokin Gandun Daji (APCU) da ke yankin Janbulo a Ƙaramar Hukumar Gwale ta jihar daga yunƙurin mayar da shi mallakar masu zaman kansu. Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Ɗahir M. Hashim ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano, ranar Juma’a. Ya ce, gwamnatin jihar na goyon bayan Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, hukumomin NAGGW, NESREA da APCU wajen kare wannan muhimmiyar cibiyar muhalli ta ƙasa daga masu zaman kansu. Dakta Hashim…
Read More

Majalisar Wakilai ta bankaɗo yadda aka naɗa Tinubu, Akume, Wike da wasu a matsayin amintattun hukumar bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin wucin-gadi kan binciken badaƙalar hukumar bogi (PFIPC) na Majalisar Wakilai, ya bayyana cewa wasu manyan jami'an gwamnati sun kasance amintattun hukumar gudanarwarta duk da tambayoyi akan halascinta da dokance. Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi ne ya bayyana hakan a wata hirar bincike a ranar Alhamis, inda 'yan majalisa suka ƙalubalanci Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), Shehu Mohammed kan amincewa da bayar da alunan lamba na ababen hawa guda bakwai da aka danganta su da hukumar. Gagdi ya ce, waɗanda aka zayyano a matsayin amintattun sun haɗa da Shugaba Bola Tinubu, Sakataren Gwamnatin…
Read More

Atiku ya tayar da ƙura bisa shigar wani kuɗi asusun bankinsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan wasu kuɗaɗe da aka tura cikin ɗaya daga cikin asusunsa na sirri ba tare da saninsa ko amincewarsa ba. A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Juma'a, an ce wani mutum da ba a san ko wanene ba ne ya tura kuɗin tare da rubuta cewa: "Contribution Electioneering Campaign." Atiku ya ce ba shi ko tawagarsa suka nemi ko suka amince da wannan kuɗi ba, yana mai cewa abin ya tayar da…
Read More

Zaɓen Osun: Davido da tsohon hadimin Buhari sun yi musayar yawu a kafar sadarwa ta zamani

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fitaccen mawakin Nijeriya, David Adeleke da aka fisani da Davido da tsohon hadimin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan lamuran kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, sun tayar da hazo a Soshiyal Mediya inda suka yi musayar kalamai masu zafi a shafin X. Wannan al'amari ya janyo hankalin jama’a musamman ganin yadda ba a saba ganin irin haka ba tsakanin mawaƙi ɗan kudu da ɗan siyasa daga arewacin Nijeriya. Al'amarin ya samo asali ne a lokacin da aka ruwaito Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta sanya wa asusun gwamnatin Jihar…
Read More