Babaji

5684 Posts

Zamfara: Gwamna Lawal ya je Bunguɗu ta’aziyyar harin ‘yan bindiga cikin aniyarsa ta yaƙi da ta’addanci

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa ko yin sulhu da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba, yana mai jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da suka dace domin murƙushe matsalar rashin tsaro a jihar. A ranar Alhamis, gwamnan ya kai ziyarar jaje Ƙaramar Hukumar Bungudu, domin ta'aziyya ga iyalan waɗanda harin 'yan bindiga ya shafa, da Masarautar Bungudu, da kuma al'ummar yankin baki ɗaya. Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, ziyarar ta fara…
Read More

‘Yan bindiga sun tsere sun bar dabbobi 452 da suka sace bayan musayar wuta da sojoji a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro a Jihar Sakkwato sun yi nasarar daƙile wasu hare-hare biyu a ƙananan hukumomin Shagari da Rabah, lamarin da ya tilasta wa maharan sakin wasu dabbobi guda 452 da suka sace bayan musayar wuta da haɗakar tawagar jami'an tsaro. An gudanar da atisayen ne a daren Talata wayewar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar ƙwato ɗaruruwan dabbobi da aka sace bayan 'yan bindigar sun tsere zuwa bayan gari. Jami'in Hulɗa da Jama’ar rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa'i ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis. A…
Read More

Tiriliyan N1.16 tallafin fetur ya lanƙwame a 2021 – Hukumar RMAFC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Shugaban Hukumar kula da Lamuran Tattara Kuɗaɗen shiga, Rabawa da Kasafi (RMAFC), Dakta Mohammed Bello Shehu ya ce Nijeriya ta kashe jimillar Naira tiriliyan 1.16 a tallafin fetur a shekarar 2021, kamar yadda aka zaftare tiriliyan N1.20 daga kuɗaɗen da aka samu sakamakon siyar da ɗanyen mai. Bello Shehu ya bayyana haka ne a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Al'umma (SPAC), wanda aka ɗora wa alhakin bincike kan rahotannin kuɗaɗen masana'antar mai da gas da Shirin Masana'antun Fitarwa Na Nijeriya (NEITI) ya gudanar. Ya ce, baya ga tallafin fetur, an…
Read More

‘Yan takara 334 sun wakilci ƙasashe a musabaƙar ƙasa-da-ƙasa ta Sarki Abdulaziz a Makkah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An fara gudanar da karatun Musabƙar Al-Ƙur'ani Mai Girma na Sarki Abdulaziz na Ƙasa-da-ƙasa karo na 46 a Makkah, Saudiyya, inda aka samu jimillar 'yan takara 334 da suka ƙunshi maza da mata daga ƙasashe 133 da suka halarta. Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Alhamis aka fara gasar a ƙarƙashin jagorancin Masallatai biyu Masu Alfarma na Sarki Salman, wadda Ma'aikatar Harkokin Addinin, Kira da Kariya ta ƙasar ta shirya. A ranar 6 ga watan Rabi Al-Awwal (19 ga Agusta) ne za a kammala gasar, wadda ta samu adadin 'yan takara mafi yawa tun…
Read More

An maka tsohon jami’in DSS a kotu kan zargin zama mamban IPOB

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta gurfanar da ɗaya daga cikin tsofaffin jami’anta mai suna Nwaogu Ezeakolam a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin sa da danganta kansa da ƙungiyar ta'addanci ta 'yan fafutukar kafa ƙasar Biafara IPOB. Rahotanni sun bayyana cewa, Daraktan kula da Shari'o'in Gwamnatin Tarayya (DPPF), Rotimi Oyedepo ya shigar da ƙarar, inda aka gurfanar da Ezeakolam a gaban Mai Shari'a Mohammed Umar bisa tuhumarsa da hannu a laifuka huɗu na zargin zama mamban IPOB da kuma wasu da suka saɓa wa dokokin haramcin ta'addanci na 2022…
Read More

Kano: Ɗan majalisa ya ƙaddamar da tashar lantarki a Bichi don bunƙasa sana’o’i

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Bichi daga Jihar Kano, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, ya ƙaddamar da buɗe tashar wutar lantarki da ake kira Farno-farno a ƙaramar hukumar. A sanarwar da Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce ya bayyana shekaru huɗu da suka wuce suke ta fafutukar yadda za a samar da tsayayyiyar wutarlantarkin a garuruwan mazaɓun yamma a garin Bichin, duba da ƙaruwar yawan jama'ar mazaɓun a halin yanzu, da hakan ya janyo matsalar rashin samun wuta yadda yakamata a yankunan. Mazaɓun da suka haɗa da; Ɗanzabuwa, Ƙyalli, Ƙauƙau da kuma…
Read More

Abin fashewa ya tarwatse a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a yankin Gadar Apo na Abuja sun shiga firgici a daren Alhamis wayewar Juma'a bayan ɓullar rahotannin tarwatsewar wani abin fashewa a kusa da gidan man Shafa, kusa da Otel ɗin Rita Lori da ke Garki. Wani shaida ya bayyana cewa ya ce ƙarar fashewar wani abu a lokuta mabambanta har sau bakwai, inda da fari ya yi zaton ko bom ne. An ruwaito cewa al'amarin ya faru ne a kuaa da gidan man, wanda ke haɗa jama'a, lamarin da ya haifar da tsoro da tilasta wa masi ababen hawa da mazauna yankin…
Read More

ICPC ta miƙa wa Tinubu rahoton binciken badaƙalar hukumar bogi, ta shawarci a gurfanar da Adeyemi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta damƙa rahotonta na wucin-gadi ga Shugaba Bola Tinubu kan binciken da ta gudanar akan badaƙalar ƙagaggiyar hukumar nan ta bogi (PFIPC), inda ta bayar da shawarar a gurfanar da wanda aka zarga cewa shi ne Darakta-Janar, Adeniyi Adeyemi. Shugaban ICPC, Musa Aliyu ya bayyana haka a ranar Alhamis bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kwana 30 da shugaban ya umarci hukumar yaƙi da rashawan da ta gudanar da cikakken bincike akan zargin badaƙalar PFIPC. A cewar Aliyu, binciken ya…
Read More

Shettima ya je hutu a karon fari bayan shekara uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai fara hutun mako biyu daga ranar Alhamis, 6 ga watan Agusta, 2026 bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince masa, lamarin da ke nuna karon farko da irin haka ya faru tun bayan hawansu kan karagar mulki a shekarar 2023. Wannan hutu zai ba wa mataimakin shugaban ƙasar damar yin amfani da lokacin wajen yin nazari da kuma sararawa domin sabunta karsashinsa na cigaba da hidimta wa ƙasa da kuma kimtsa wa shirye-shiryen zango na gaba na gwamnatin nasu. Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya umarci EFCC ta buɗe asusun bankin gwamnatin Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gaggauta neman kotu ta soke umarnin rufe asusun gwamnatin Jihar Osun da kuma daina ɗaukar dukkan wani mataki akan jihar game da al'amarin. Tinubu ya bayar da wannan umarni ne a wata takarda da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026, inda ya ce ya ji takaici akan lokacin da hukumar ta ɗauki matakin, yana mai cewa ba ya inkarin ikon da dokar ƙasa ta ba EFCC na aiwatar da hukuncin saidai bai dace…
Read More