06
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta kammala shirin kawo karshen aikin buga fasfuna a ofisoshinta dake jihohin Nijeriya, inda yanzu ta mayar da tsarin bugawa a cibiya guda da ke hedikwatarta Abuja. NIS ta ɗauki wannan mataki ne da nufin ƙarfafa tsaro, inganta harkar gudanarwa da kuma zamanantar da tsarin samar da fasfo a Nijeriya. A wata sanarwa da jami'inta na hulɗa da jama'a, Akinsola Akinlabi ya fitar a ranar Laraba, ya ce masu neman samun fasfo za su cigaba da zuwa ofisoshin da suke so, yan ai tabbatar da cewa cibiyoyin…
