Babaji

5684 Posts

Ambaliya ta yi ajalin jami’in tsaro da matashi a Yobe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mamakon ruwan sama da aka zabga a sassan Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ya haddasa ambaliyar da ta yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu. Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) ta tabbatar da faruwar al'amarin a wata takarda da ta fitar a ranar Talata. Ta ce, waɗanda iftila'in ya yi ajalin nasu sune wani jami'in tsaro mai suna Mallam Matari da wani matashi ɗan kimanin shekaru 18, Abba Kyari, waɗanda ambaliya ta halakar a yankin Pompmari. A cewar hukumar, ambaliyar ta auku ne a Malari, Pompomari da kuma wasu yankunan kewayensu bayan wani ruwan…
Read More

Gwamnan Kaduna ya karɓi baƙuncin matar marigayi Edwin Achi da mijin Ummulkhairi da aka halaka a Maraba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya karɓi baƙuncin mijin matar nan mai suna Ummulkhairi Aliyu da aka halaka a yankin Maraban Jos, wato Malam Usman Aliyu da kuma matar marigayi Ven. Edwin Achi, Misis Sarah Achi. Uba Sani ya karɓi baƙuncin nasu ne a gidan gwamnatin jihar a lokacin da suke je nuna godiyarsu a gare shi bisa tallafa musu. Yayin da suka samu rakiyar babban faston Kaduna, Reberen Timothy Yahaya da Sheikh Haliru Maraya, mutane biyun sun yi godiya ga gwamnan bisa cika alƙawuran da ya musu na samar…
Read More

Mayaƙan ISWAP biyar ciki har da Larabawa sun rasu yayin ƙera boma-bomai a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mayaƙan ƙungiyar ISWAP guda biyar ciki har da wani da ake zargin jami'in lafiya ne da wasu huɗu waɗanda ƙwararru ne wajen ƙera ababen fashewa (IEDs), sun rasu a lokacin da suke ƙoƙarin haɗa boma-bomai a Ƙaramar Hukumar Marte ta Jihar Borno. A ranar Talata masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ya sanar da faruwar al'amarin, wanda ya auku a ƙauyen Maina Daya da ke tsakanin Sabon Tumbu da Jubilaram, kusan kilomita 29 daga gabashin Ƙaramar Hukumar Monguno da ke Borno. A cewar majiyoyi, al'amarin ya yi ajalin Usman Ɗan Fulani da aka bayyana a…
Read More

Ƙungiyar Next Frontiers Hub Initiative ta gana da malamai da sarakuna kan inganta al’umma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar kula da lamuran inganta rayuwar al'umma ta Next Frontiers Hub Initiative (NFHI) ta jagoranci taron tattaunawa da haɗin-gwiwa wanda ya ƙunshi malamai, sarakunan gargajiya da sauran jagororin al'umma da nufin ƙara wa juna sani kan al'amuran da suka shafi ci-gaban al'umma. An gudanar da taron ne a ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2026 a wani ɗakin taro a Birnin Tarayya Abuja. A wata sanarwa da Sakatarenta, Ɗahiru Muhammad ya fitar, NFHI ta ce ta taron wani fage ne na tattaunawa, haɗin-gwiwa da bayyana dabaru akan lamuran kuɗi, rage talauci, inganta matasa da…
Read More

‘Yan yahoo sun saci bayanan kwastomomin Bankin Zenith bayan aikata kutse

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bankin Zenith ya tabbatar da cewa ya fuskanci kutsen na'ura a kwanan nan sakamakon wasu 'yan yahoo sun samu damar shiga matattarar bayanan kwastomominsa duk da cewa ya tabbatar musu da cewa hulɗa da shi da fagagensa na dijital za su cigaba da aiki bisa sanya ido da tsaro. Rahotanni sun ce bankin ya bayyana cewa kutsen wani ɓangare ne na hare-haren yanar gizo da ake kai wa cibiyoyi a fannoni daban-daban. A cewar Zenith, kutsen ya taƙaitu ne kaɗai wajen samun bayanan da suka shafi adireshin Imel da lambobin waya, yana mai cewa…
Read More

Sojoji sun kama mutum huɗu bisa zargin kai wa Boko Haram da ISWAP magani da wasu ababe a Borno da Yobe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai da ke aiki a shiyyar Arewa maso Gabas, sun yi nasarar kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aiki tare da mayaƙan Boko Haram da ISWAP wajen kai musu wasu kayayyakin amfanin yau da kullum. Sojojin sun kuma kama wasu mutane 20 da ake zargin iyalan mayaƙan Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jiha ne da suka tsere daga sansaninsu a Ƙaramar Hukumar Konduga ta Jihar Borno. Kyaftin Mohammed Goni, jami'in yaɗa labaran dakarun na riƙo ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a yau Talata.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya ƙara wa sojoji albashi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da yi wa albashin jami'an sojoji ƙari. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Ministan Tsaro Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya ce kwanan nan Shugaban zai yi ƙarin albashi ga dakarun soji. A ƙarƙashin sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Satumba, jami'an da ke muƙami sama da kanal za su samu ƙarin kaso 30 daga ainihin abin da suke karɓa a wata yayin da daga kanal zuwa ƙasa kuma za su amfani da tagomashin ƙarin kaso 50. Sai kuma masu muƙamin 'Private'…
Read More

Real Madrid na shirin koma wa tattaunawa da Vinicius wanda Arsenal ke kwaɗayin saye

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Zakaran ɗan wasan Real Madrid ta ƙasar Sifaniya, Vinicius Jr na shirin cigaba da tattaunawa kan batun kwantaragi da ƙungiyar a wannan makon, yayin da wadda ta lashe Premier League a kakar wasan da ya gabata, Arsenal ke cigaba da nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan gaban. Arsenal ta zaɓi ɗan Brazil ɗin a matsayin wanda take fatan saye don ƙara wa gefen hagunta ƙarfi matuƙar Madrid ta gaza daidaitawa da shi. Saidai duk da raɗe-raɗin komawar Vini Arsenal ya ɗauki hankalin magoya baya, har yanzu akwai rashin tabbas na yiwuwar komawarsa a wannan bazarar.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar dokokin Kano ta dakatar da ciyamomin ƙananan hukumomi 3 na wata uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bebeji, Rogo da Ɓagwai na jihar daga aiki na tsawon watanni uku. Mai taimaka wa gwamnan jihar na Musamman akan harkokin Yaɗa labarai na Zamani, Ibrahim Adam ne ya sanar da haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook. "Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da ciyamomin ƙananan hukumomin Bebeji, Rogo da Ɓagwai daga aiki na tsawon watanni uku", kamar yadda ya rubuta a shafin nasa. A lokacin aikin haɗa wannan rahoto, babu wani saƙo a hukumance da aka samu akan…
Read More

An zargi sojoji da harbin ɗan kasuwa yayin sintiri a Mubin Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a garin Mubi na Jihar Adamawa sun shiga alhini bayan zargin jami'in soja da harbin wani ɗan kasuwa mai suna Suleiman Abi, a lokacin da suke gudanar da aikin sintiri a Ƙaramar Hukumar Mubi ta Arewa. Al'amarin ya auku ne da misalin 8:40 na ranar Lahadi, wanda ya haifar da alla-wadai da gudanar da zanga-zangar lumana daga 'yan yankin kan kira na a tabbatar da gaskiya da adalci a kai. A cewar mazauna, al'amarin ya faru ne a lokacin da mutumin yake tuƙa babur ɗinsa na laturoni, inda ya gano cewa sojojin suna…
Read More