Babaji

5684 Posts

Sai da aka biya miliyan N50 kafin sako alƙalin Kebbi, inji iyalansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyalan Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruk Hassan Bunza da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi a gidansa, sun tabbatar da cewa sai da aka biya kuɗin fansa Naira miliyan 50 kafin aka sako shi. Rahotanni sun bayyana cewa, Alƙali Bunza ya shaƙi iskar 'yanci ne a ranar Litinin bayan shafe kwanaki takwas a hannun 'yan bindigar da suak sace shi a safiyar ranar Lahadi, 26 ga Yuli, lokacin da suka je gidansa da ke Ƙaramar Hukumar Bunza a jihar Kebbi. Wani ɗan gidan alƙalin da ya nemi a sakaye…
Read More

ICPC ta kammala binciken badaƙalar PFIPC, Majalisar Wakilai za ta bayyana sakamako wannan makon

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta kammala bincikenta akan cece-kucen badaƙalar wanzuwar Hukumar kula da Ci-gaban Zuba Jari na Ƙasashen Waje ta Shugaban ƙasa (PFIPC). Haka kuma, kwamitin binciken al'amarin na wucin-gadi na Majalisar Wakilai ya ce zai ba wa 'yan Nijeriya ba'asin sakamakon binciken a wannan mako gabanin miƙa rahotonsa ga majalisar, bayan tsawon makonni ana binciken akanHukumar. A ranar 7 ga Yuli, 2026 ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC da ta gudanar da cikakken bincike akan PFIPC cikin kwanaki 30 tare da bayar da rahotonta domin gano haƙiƙanin…
Read More

An kama soja kan roƙar kuɗi a TikTok sanye da kaki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An kama wani soja da ke aiki a sashen dakarun sama na Nigerian Army Aviation Hangar a Minnan Jihar Neja, sakamakon bayyanar wani bidiyon TikTok da aka gan sa a ciki yana roƙon wani sanannen ɗan Soshiyal Mediya mai sun King Pedro kuɗi a lokacin da yake sanye da kakin sojoji a jikinsa. Rahotanni sun bayyana cewa, sojan ya bayyana ne a wani shiri na kai tsaye a kafar TikTok inda ya nemi taimakon kuɗi saboda halin ƙuncin da yake ciki, lamarin da ya sa hukumomin soja ɗaukar matakin kama shi domin gudanar da…
Read More

Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙudirin kula da kuɗin karatu a makarantu masu zaman kansu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta kammala karatun ƙarshe akan ƙudirin kafa dokar kula da kuɗin karatu da ake biya a makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar, inda ta samar da sababbin matakai da nufin bayar da kariya ga iyaye wajen biyan kuɗi sama da kima sakamakon ƙare-ƙare da kuma ƙarfafa matakin sanya ido a cibiyoyin ilimi. Ƙudirin, wanda aka yi laƙabi da "Kano State Private and Voluntary Institutions Board (Amendment) Bill, 2026", na neman a bunƙasa harkar kulawa da lamuran makarantu masu zaman kansu yayin tabbatar da tsare gaskiya…
Read More

Sanata Rufa’i Hanga ya fice daga NDC a hukumance

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Rufa'i Hanga, ya yi fice daga jam'iyyar NDC a hukumance, lamarin da ya kawo ƙarshen tarayyarsa da ita a nan take. Rahotanni sun nuna cewa, Sanata Hanga, wanda shi kaɗai ne sanatan NDC daga arewacin Nijeriya kuma mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye majalisar, ya sanar da murabus ɗin nasa ne a wata takarda da ke ɗauke da 3 ga Agusta, 2026, kuma ya gabatar da ita ga shugaban jam'iyyar na Gundumar Najeria da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Ɗan Majalisar ya ce, ya ɗauki…
Read More

Majalisar Dattawa ta ba NNPCL, CBN da NDDC sa’o’i 72 su bayyana a gabanta kan zargin coje a rahoton kuɗi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Majalisar Dattawa akan Asusun Al'umma, ya bayar da wa'adin kwana uku ga Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Babban Bankin Nijeriya (CBN), Hukumar kula da Ci-gaban yankin Neja-Delta (NDDC), Hukumar kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC) da wasu hukumomi da su bayyana a gabansa sakamakon rashin amsa gayyatarsa a lokuta mabambanta game da warware matsalolin rahotannin kuɗaɗe. An bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin a lokacin da kwamitin ya gabatar da wani zama ba tare da hukumomin sun je gabansa ba kuma babu wani bayani a hukumance game…
Read More

Babu hidimar ƙasa ga wanda NERD ba ta tantance ba – NYSC ga ɗalibai masu kammala digiri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Harkokin Ɗalibai Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), ta gargaɗi masu shirin fara hidima kan cewa ba za a ba su damar farawa ba har sai sun samu tantancewa daga Cibiyar Rajistar Tattara Bayanai ta Laturoni ta Ƙasa (NERD). Rahotanni sun bayyana cewa, gargaɗin na zuwa ne yayin da hukumar take cigaba da shirin karɓar tawagar ɗalibai na sabon rukuni yayin da take kuma ɗaukar matakan tabbatar da tsaronsu yayin tafiye-tafiye zuwa sansanoninsu. A wata sanarwa da ta wallafa ta kafar X a ranar Litinin, NYSC ta sanar da cewa daga…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta ayyana 3 ga Satumba a matsayin ranar ƙarshe ta miƙa ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, a ranar 3 ga watan Satumba, 2026 ne za a miƙa wa Shugaba Bola Tinubu ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi domin yin nazari a kansa. Shugaban Ma’aikatan fadar, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana haka, inda ya ce an tsara aikin ne cikin makonni bakwai domin kammala tsarin doka da zai bayar da damar aiwatar da shirin ‘yan sandan jihohin. Ya ce, bayan shugaban ƙasa ya duba kuma ya amince da ƙudirin, za a gudanar da aikin tuntuɓar al’umma kafin a sake gabatar da shi a gaban Majalisar…
Read More

2027: Tsohon Sufeto-Janar, Sulaiman Abba ya jaddada aniyar zama sanata a PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Sufeto-Janar na Rundunar 'Yan sandan Nijeriya, Alhaji Sulaiman Abba, ya nanata aniyarsa ta neman zama sanata a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP daga Jihar Jigawa a yayin babban zaɓen shekarar 2027. Sulaiman Abba ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce har yanzu yana da muradin cigaba da hidimta wa al'umma ta hanyar riƙe muƙaman siyasa. A cewarsa, rashin ba shi damar tsaya wa takara a jam'iyya mai mulki (APC) ya yi tasiri wajen ɗaukar matakin sauya sheƙarsa zuwa PDP domin dacewa da kyawawan…
Read More

Za mu dakatar da ƙaddamar da sabbin hare-hare akan Iran, inji Trump

Daga BEL A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa, Amurka da Isra'ila sun amince su dakatar da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran matuƙar aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu cikin gaggawa. Trump ya ce, ya yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, da kuma tattaunawar da Iram ɗin ta yi da Saudiyya, Pakistan da Turkiyya domin rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Saidai Iran ta musanta iƙirarin cewa ta roƙi Amurka ta dakatar da hare-hare, tana mai cewa kalaman na Trump ba…
Read More