03
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar wani mamakon ruwan da aka zabga a sassan ƙananan hukumomin Damaturu, Nguru, Machina da Bursari na Jihar Yobe ya haddasa ambaliya, lamarin da ya yi sanadiyyar damejin wasu gidaje da kai agajin gaggawa daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA). SEMA ta sanar da batun a wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, 2 ga Agusta, 2026. Blueprint Manhaja ta gano cewa hukumar ta samu kiran buƙatar agajin gaggawa daga jagororin al'umma hukumomin tsaro da hukumomin ƙananan hukumomi bayan ruwan saman da ya haɗe ƙauyuka da dama. Yankunan…
