Babaji

5684 Posts

2027: INEC ta wallafa cikakken jaddawalin ‘yan takarar shugaban ƙasa babu sunan Jonathan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta wallafa sunaye da bayanai akan 'yan takarar shugaban ƙasa guda 19 da abokan tafiyarsu daga jam'iyyu daban-daban domin karawa a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe, matakin da ya bayar da dama a gare su su fara yawon yaƙin neman zaɓe a ranar 19 ga Agusta. Wannan mataki wani ɓangare ne na biyayya ga Sashe ma 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya hukunta wa hukumar ta wallafa sunayen 'yan takara da suka ƙunshi bayanai na kai-tsaye akansu. Hakan zai ba wa al'umma damar yin nazari…
Read More

Shugabanci na gari ‘yan ƙasa suke so ba gina gadoji ba – Tinubu ga gwamnoni

Shugaba Bola Tinubu ya kirayi gwamnonin jihohi da su daina gina gadar sama a jihohinsu, a madadin haka su mayar da hankali wajen sarrafa kuɗaɗen da aka ware musu na tarayya zuwa bunƙasa hanyoyin sadarwa da hanyoyi da za su inganta yanayin rayuwa da cigaba al'umma da jihohinsu. Tinubu ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar sarakunan gargajiya daga Jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Olubadan na Masarautar Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, waɗanda suka je domin taya shi murna kan nasarar ceto ɗalibai da malaman makaranta da aka sace a Karamar Hukumar Oriire bayan kwana 56 a…
Read More

Ka daina ba wa gwamnoni kuɗaɗen cire tallafin fetur – Jigon APC ga Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jigon jam'iyyar APC a Jihar Neja, Hon. Jonathan Vatsa ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da kuɗaɗen da gwamnati ta samu a sakamakon cire tallafin man fetur wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba a madadin ba wa gwamnoni. Waɗannan kalamai na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohin Nijeriya da su daina amfani da kuɗaɗen al'umma wajen gina manyan gadoji. Babban ɗan APCn, wanda shi ne sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na farko, ya bayyana haka ne a wata hira da 'yan jarida a jiya…
Read More

Ganduje ya sasanta rikicin ƙungiyar kansilolin APC ta ƙasa a matsayin Uban Ƙungiya bayan umarnin Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasarar sulhunta rikicin da ke tsakanin 'ya'yan Gamayyar Ƙungiyoyi Huɗu na Kansilolin APC ta Ƙasa ta 'Four Nigerian APC Councilors' Forum' bayan tsawon lokaci. Bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi umarnin shiga tsakani, Ganduje ya cimma haka ne ta hanyar zama da wakilan ƙungiyar, wadda akan haka ne ta gudanar da zama a ranar Alhamis, 29 ga Yuli, 2026 tare da fitar da sababbin matakan gudanarwa. A yayin haka ne ta cimma matsayar naɗa tsohon…
Read More

Fitaccen daraktan Kannywood, Aminu Saira ya ƙara aure

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma’a shahararren mai shirya fim kuma darakta, Mallam Aminu Saira ya auri mata ta biyu. An gudanar da ɗaurin auren ne a garin Azare da ke Jihar Bauchi a wani yanayi na farin ciki da san-barka. Taron ɗaurin auren ya haɗa mutane da dama ciki har da abokan aiki, masoya da masu ruwa da tsaki a harkar finafinai a sassan Arewacin Nijeriya, waɗanda suka taya daraktan murna bisa ƙaruwar da ya samu da kuma addu'o'i daga al'umma ta kafar Soshiyal Mediya. Bayan ɗaurin auren, an yi ta yaɗa hotunan Aminu Saira da…
Read More

Sojoji sun daƙile yunƙurin garkuwa na Boko Haram, sun ceto fararen hula 31 a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabas sun yi nasarar daƙile wani harin 'yan ta'adda na yunƙurin garkuwa, inda suka ceto mutane 31 a atisayen, wanda aka ƙaddamar a yankin titin Buratai zuwa Kamuya da ke Ƙaramar Hukumar Biu a Jihar Borno. Atisayen ya kuma yi sanadiyyar ƙwato motocin fararen hula guda huɗu da baburan da 'yan ta'addar suka tsere suka bar su bayan musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu. Jam'in yaɗa labaran sojojin na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni ne ya sanar da ci-gaban a wata takarda da ya fitar, inda…
Read More

Ai ba a sake rubuta tarihi – Martanin Atiku ga Obasanjo kan nadamar shugabancinsu tare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi martani da babbar murya ga tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo kan kalamansa na kwanan nan, yana mai bayyana su a matsayin wata rashin nasara ta yunƙurin sake rubuta tarihi. Ya ce, babu wata buƙata ta raɗin kai da za ta iya goge raɗaɗin matsayarsa ta ƙin amincewa ajandar samar da tsarin wa'adi na uku ko wata rawa da ya taka a harkar siyasar Obasanjo. Martanin Atikun ya biyo bayan sukar Obasanjo ne akansa yayin wata hira, yana mai cewa tarihi ne zai yi…
Read More

A shirye muke mu tattauna da gwamnati – Boko Haram ga iyalan mutane 50 da ta sace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shigo tsakani domin a tattaunawa akan sako sama da mazaunan Jihar Borno 50 da aka yi garkuwa da su wajen sanya wani ɗan jarida a matsayin ɗan tsakani. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa ba ta manta da ɗaliban makarantar firamare da sakandare ta Askira-Uba da aka sace ba a ranar 15 ga watan Mayu, tana mai cewa dakarun tsaro na aiki tuƙuru wajen ganin an ceto…
Read More

Ɗaukar ka a matsayin abokin tafiya shi ne babban kuskurena – Obasanjo ga Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana matakinsa na ɗaukar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin abokin tafiyarsa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999 a matsayin mafi girman kuskure a shugabancinsa. Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a Legas, a lokacin da yake tattaunawa da daɗaɗɗen ɗan fafutuka, Charles Oputa da aka fi sani da Charly Boy, a wani taron Gidauniyar Charly Boy da aka shirya domin karrama Marigayi Chukwudifu Oputa. Tsohon shugaban ƙasar, wanda ya jagoranci Nijeriya tare da Atiku a tsakanin 1999 da 2007, ya ce kowane shugaba…
Read More

2027: INEC ta wallafa bayanan Tinubu, Obi, Atiku da wasu ‘yan takara ga al’umma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fara wallafa bayanan 'yan takarar da jam'iyyun siyasa suka miƙa mata domin shiga takara a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Ta ce, matakin biyayya ne ga hukunce-hukuncen Dokar Zaɓe ta 2026. Haka kuma, ya yi daidai da jaddawali da tsare-tsaren zaɓen da ta fitar a kwanan nan daga takardun da 'yan takarar kujerar shugaban ƙasa suka gabatar domin zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 16 ga Junairu 2027. A sanarwar da ta fitar a ranar Asabar, INEC ta ce ta wallafa bayanan…
Read More