Babaji

5684 Posts

Basaraken Ibadan, Lekan Alabi ya rasu a shekara 76

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Cif Lekan Alabi, wanda shi ne Abese Olubadan na Masarautar Ibadan, ya rasu bayan shafe shekaru 76 a duniya. Marigayi Alabi, wanda tsohon ɗan jarida kuma tsohon sakataren yaɗa labaran tsofaffin gwamnonin Jihar Oyo ne, ya rasu ne a safiyar yau Asabar. Mai taimaka wa Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja akan harkokin yaɗa labarai, Adeola Oloko ne ya sanar da labarin rasuwar a wata takarda da ya fitar a Ibadan, babban birnin Oyo. Ya bayyana cewa, marigayin ya rasu ne a Legas kuma za a yi jana'izarsa a gobe Lahadi kamar yadda addinin Musulunci…
Read More

2027: INEC ta ƙi karɓar sunan Jonathan a matsayin ɗan takarar PDP da tsgin su Turaki ya gabatar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi watsi da miƙa sunan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan a gare ta da tsagin jagorancin jam'iyyar PDP na su Kabiru Turaki ya yi ta wani kundi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027, tana mai cewa za a iya yin hakan ne kaɗai ta sahihin shafinta na yanar gizo. Hakan na zuwa ne bayan da tsagin a ranar Juma’a ya tirje akan ya miƙa wa hukumar suna Jonathan da wasu a matsayin sunayen 'yan takarar jam'iyyar a zaɓen na 2027 da ke…
Read More

Sojoji sun ceto mutum 14 da aka sace a babban titin Legas zuwa Benin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na Birget ta 4 na Rundunar Sojin Nijeriya da ke Sashe na 2, sun yi nasarar ceto wasu mutane su 14 da aka yi garkuwa da su a yankin babban titin Legas zuwa Benin a Ƙaramar Hukumar Ovia ta Gabas da ke Jihar Edo, a wani ɓangare na Atisayen Wabaizigan. A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Kennedy Anyanwu ya aike wa manema labarai, ya ce an gudanar da atisayen ne bayan al'amarin garkuwar ya faru da misalin ƙarfe 9:30 na daren Alhamis, 30 ga Yuli, 2026. Ya…
Read More

Sarki Sanusi ya jinjina wa CBN yayin da ya nuna goyon baya ga gyare-gyaren tattali na Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya nuna amincewa da goyon bayansa akan gyare-gyaren al'amuran tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samar, inda ya yaba wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) bisa ɗaukar matakan dawo da ɗorewa al'amura a ƙasar. Sarkin, wanda tsohon gwamnan CBN ne, ya ce ƙasar ta farfaɗo daga halin taɓarɓarewar lamuran tattalin arziƙi sakamakon warware matsalolin samar da wadatar kuɗi, rage matsin hauhawar farashi da ɗorewar matakin canjin kuɗi. Mai Martaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin akan fannin tattali, inda ya ce ba shi da…
Read More

Kano: ‘Yan sanda sun ceto ɗan shekara 9 bayan kusan wata da sace shi yayin da aka kama mutum 10 da ake zargi

Rundunar 'yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta ceto wani yaro ɗan shekara tara mai Ubaiyu Muhammad Sammani bayan tsawon makonni huɗu da yin garkuwa da shi. Haka kuma, rundunar ta kama mutum 10 da ake zargi da hannu a sace yaron, waɗanda suka haɗa da maza guda tara da mace ɗaya. Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce masu garkuwar sun nemi a biya su dala 30,000 kafin su saki yaron, wanda ke zaune a unguwar Rimin Kebbe cikin ƙoshin lafiya. Ya ce, jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane ne suka gudanar da atisayen pceton a…
Read More

Sojoji sun ceto mutane 397 yayin da ‘yan ta’adda 57 suka miƙa wuya a Yuli – DHQ

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta sanar da cewa jami'an sojoji sun yi nasarar ceto mutane 397 da aka yi garkuwa da su a lokacin atisaye daban-daban a watan Yuli, yayin da 'yan ta'adda 57 da iyalansu suka miƙa wuya a ƙoƙarin daƙile miyagun ayyuka a sassan Nijeriya. Daraktan yaɗa labara na hedikwatar, Manjo-Janar Michael Onoja ne ya sanar da nasarorin a ranar Juma'a yayin gabatar da sakamakon ayyukan sojoji na watan Yuli. A cewarsa, sojoji a rassa daban-daban sun halaka jimillar 'yan ta'adda da wasu ɓarayi guda 102, sun kama mutane 345 da ake…
Read More

Alƙalin alƙalai ta haramta amfani da kalmar ‘barrister’ a ayyukan Kotun Ƙoli

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Alƙalin alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta umarci lauyoyi da jami'an kotu da su daina amfani da laƙabin 'Barrister' gabanin ainihin sunayensu a dukkan ayyukan da suka shafin Kotun Ƙoli a hukumance. Manhaja ta ruwaito cewa, umarnin da ƙunshe ne a wata takarda da ke ɗauke da kwanan wata 13 ga Yuli, 2026 kuma Babban Rajistiran kotun, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu. Takardar, wadda aka fitar da ita musamman don jami'an shari'a, rajistirorin kotu da lauyoyi, ta bayyana cewa umarnin ya fara aiki ne a nan take a matsayin wani ɓangare…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta wallafa yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin fetur, inji minista

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce kwanan nan za ta fitar da cikakken bayani akan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur da kuma gyaran tsare-tsaren canjin kuɗi, domin amsa tambayoyin da jama'a ke yi kan inda kuɗaɗen suka je. Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin ta kuma ce an tafiyar da kuɗaɗen tallafin da na gyaran tsare-tsaren canjin kuɗi ne ta hanyar warware basusukan gudanarwa da ƙarin adadin kashe-kashen gwamnati, yayin da jami'an gwamnati ke cigaba da bayar da kariya ga gyare-gyaren wajen danganta su da tsadar rayuwa. Ministan Kuɗi kuma…
Read More

Tinubu ya rushe kwamitin shugaban ƙasa kan kadarorin gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da gaggauta soke Kwamitin Aiwatarwa na Shugaban ƙasa (PIC) akan harkokin gudanar da kadarorin Gwamnatin Tarayya. Tinubu ya ce, dukkan wasu al'amura da suka shafi kwamitin daga yanzu, za su koma ƙarƙashin kulawar Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN). A ranar 22 ga watan Maris, 2001 ne Majalisar Zartarwar ta amince da samar da kwamitin tuntuɓa domin samar da farar takardar da za ta taimaka wajen aiwatar da shawarwarinta akan al'amarin. Kwamitin ya yi aiki har na tsawon watanni 21 kana ya miƙa rahotonsa. A…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta soke cire tallafin lantarki sai 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na daina biyan kuɗaɗen tallafi a fannin wutar lantarkin Nijeriya, wanda za a fara daga shekarar 2027. Ministan Lantarki Joseph Tegbe ne ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a ranar Juma'a, yayin da yake warware matsalolin da suka shafi bashi a fannin lantarkin ƙasar. Ya bayyana cewa, za a cire tallafin da kaɗan da kaɗan, yana mai tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa za a gudanar da al'amarin cikin tsari domi tabbatar da cewa sun amfana da tsarin. Minutes ya kuma jaddada aniyar gwamnatin tarayyar…
Read More