Babaji

5684 Posts

2027: An shiga ruɗani bayan PDP tsagin Turaki ya miƙa sunan Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ga INEC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsagin jagorancin kwamitin riƙo na ƙasa na jam’iyyar PDP, ƙarƙashin Tanimu Turaki, ya ce ya miƙa sunan tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Kakakin tsagin, Ini Ememobong ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce baya ga Goodluck Jonathan, sun kuma miƙa sunayen sauran 'yan takarar jam’iyyar domin shiga takara a zaɓuka daban-daban ga hukumar. Ya kuma ce wannan matakin na daga…
Read More

Jami’ai takwas sun rasu bayan motocin sojoji sun bi ta kan bom a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla sojojin Nijeriya takwas ne suka rasu bayan tawagar motocinsu ta bi ta kan wani abin fashewa da aka zargi mayaƙan ƙungiyar ISWAP da dasawa a Jihar Borno. An gano cewa, al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da dakarun Birget na 24 na Task Force a Dikwa suke koma wa sansaninsu daga Maiduguri bayan rakiyar wasu motoci da suka yi dakon kayan abinci da wasu ababe. A cewar majiyoyin sojoji kamar yadda ShaharaReporters ta ruwaito, motar yaƙi ce ke jagorantar sauran motocin a lokacin da iftila'in ya auku akan hanyar. Ta ce,…
Read More

Nijeriya na da gangar iskar gas sama da tiriliyan 200 a rumbun ajiyarta, inji Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al'umma, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Nijeriya ta mallaki sama da ganga tiriliyan 200 na albarkatun iskar gas a majiyarta, lamarin da ya sa ta shiga sahun ƙasashe masu mafi yawan arziƙin a Nahiyar Afirka. Ministan ya faɗi haka ne a ranar Alhamis a yayin taron Ƙungiyar Ci-gaban Kasuwancin AKK ta Jihar Neja (Niger State AKK Business Development Forum), wanda aka gudanar a Minna. Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya a yanzu tana iya fitarwa domin ciyar da masana'antu gaba, samar da makamashi, samar da ayyukan yi da…
Read More

Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar ranar Alhamis ne tsohon Ministan Kuɗin Nijeriya kuma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji ya rasu bayan shafe shekaru 87 a duniya. Dikkon Sakkwato, Alhaji Ya'u Dogon Daji ne ya tabbatar da labarin, inda ya ce marigayin ya yi fama da rashin lafiya na kusan wata guda, kuma ana sa ran za a yi masa sallar jana'iza a Masallacin Sultan Bello na Sakkwato kafin a binne shi a Hubbaren Shehu a jihar. Kafin rasuwarsa a wani asibitin Abuja, marigayin ya riƙe muƙamai daban-daban a gwamnatin Nijeriya a tsawon sama da shekaru 30 da…
Read More

Ancelotti ya ɗora laifin cire Brazil a gasar Kofin Duniya kan hutun shan ruwa ana tsaka da wasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kociyan Brazil, Carlo Ancelotti, ya ɗora laifin cire ƙasar da aka yi a gasar Kofin Duniya na 2026 a zagayen 'yan 16 akansa, yana mai cewa an samu ƙwacewar lissafi ne a yayin da aka je hutun shan ruwa a wasan da ta kara da Norway. Daɗaɗɗen kocin ya amince cewa matakin da ya ɗauka wajen sauya salon wasan ne ya sanya Erling Haaland ya zura ƙwallon da ya ba Norway nasara akan Brazil, kamar yadda ya bayyana a wata hira da da ESPN ta wallafa. Ya bayyana cewa, Brazil ta kasance mai jan…
Read More

‘Yan sanda sun kama sakataren gwamnati da wasu biyar kan zargin maguɗin zaɓe a Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Osun ta tabbatar da kama Sakataren Gwamnatin jihar (SSG), Teslim Igbalaye, tare da wasu mutane biyar bisa zargin su sayen ƙuri’u, mallakar kayayyakin zaɓe ba bisa ƙa’ida ba, da kuma wasu laifukan da suka shafi zaɓe gabanin zaɓen gwamnan jihar da ake shirin gudanarwa. A cewar rundunar, kamen ya biyo bayan wani samame da jami’anta suka kai wani gida da ke Oroki Estate a birnin Osogbo, bayan samun sahihan bayanan sirri. A yayin samamen, an ce an kwato Naira miliyan 4.8, katunan zaɓe na dindindin (PVCs), rajistar masu zaɓe da…
Read More

DSS ta ankarar da sojoji shirin Boko Haram na ƙaddamar da hare-hare a Adamawa da Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An shiga sabon fargaba a wasu sassan jihohin Adamawa da Borno bayan saƙon gargaɗin ankararwa da aka fitar game da shirin ƙungiyar Boko Haram na ƙaddamar da wasu hare-hare a ƙananan hukumomin Michika da Askira-Uba. Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ce ta fitar da saƙon, inda ta yi iƙirarin cewa mayaƙan ƙungiyar na shirin gudanar da atisayen hare-haren ne sakamakon zargin rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da gwamnatocin jihohin biyu. An gabatar da takardar saƙon ne mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Yuli, 2026 ga Kwamandan Birget ta 23 ta Rundunar Sojin…
Read More

Harin ‘yan bindiga a masallaci ya yi ajalin mutum bakwai da garkuwa da wasu a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane bakwai ne aka halaka yayin da aka sace wasu da dama a lokacin da wasu 'yan bindiga suka afka wa ƙauyen Tsamaye da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato. An ruwaito cewa, uku daga cikin waɗanda suka rasu an kashe su ne a masallaci yayin harin, wanda aka ƙaddamar da misalin ƙarfe 8:30 na daren Talata wayewar Laraba kuma ya ɗauki tsawon sa'o'i bakwai ba tare da tsayawa. Mazauna yankin sun ce, maharan sun kutsa yankin ne cikin adadi mai yawa, inda suka riƙa harbe-harbe tare da farmakar mutane a…
Read More

Kano: An yi wa ‘yan marasa galihu 16 auren gata a Bichi – Kwamandan Hisbah

A karo na biyu da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ke gwangwaje mata marasa ƙarfi da auren gata a ƙarƙashin Hukumar Hisba, 'yan mata guda 16 za su rabauta da irin wannan aure a Ƙaramar Hukumar Bichi. Kwamandan Hisba na yankin, Malam Murtala Safiyanu ne ya bayyana haka a yayin tattaunarwasu da Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo a ofishinsa dake Cibiyar adinin Musulunci ta ƙaramar hukumar. Ya ce, kayan da gwamnati ke ɗaukar nauyin bayarwa kama daga setin gado zuwa kayan abinci na gara, tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alƙawari, inda Ƙaramar…
Read More

Kano: Yana da kyau mu san yadda ake gudanar da asibitocinmu – Mai kishin al’umma a Bichi

Kwamitin mutane masu tasiri acikin al'umma da ke aiki a matakin ƙananan hukumomi, Reshen Ƙaramar Hukumar Bichi, wato Local Health Advocacy And Accountability Team (LHAAT) da aka samar a ƙarƙashin Ƙungiyar Intergrated Child Survival Advocacy At The Last Mile (ICSA), ya gudanar da taron sanin makamar aiki ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Yankin, Alhaji Abbas Idris Bayero, Wakilin Hakimin Bichi Galadiman Kano Alhaji Mannir Sanusi, a ofishinsa da ke Hukumar Hisba ta ƙaramar hukumar. A sanarwar da Jami'ar Yaɗa Labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, Alhaji Wakili Abbas, bisa mahimmancin lafiya ya zaburar da…
Read More