Babaji

5684 Posts

Sakkwato: Hisbah ta haramta ‘na gani ina so’ da tarukan cakuɗa maza da mata a bukukuwan aure

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hisbah a Jihar Sakkwato, ta sanar da haramta wasu taruka da al'adu da ake gudanarwa yayin bukukuwan aure a faɗin jihar. Ababen da hukumar ta haramta sun haɗa da amfani da masu jagorantar kayan sauti a taruka (DJs), gabatar da kayan "Na Gani Ina So", taron cakuɗa maza da mata da kuma yin almubazzaranci wajen siya wa amarya kyautuka, tana mai bayyana hakan a matsayin ababen da suka saɓa wa karantarwar addinin Islama. Haka kuma, hisbar ta haramta amfani da waƙar "Wazigidi" a taruka, yawo da manyan sifiku a adaidaita sahu, zaman mace…
Read More

Sojoji sun ceto shugaban kwalejin tarayya bayan daƙile yunƙurin hare-haren garkuwa a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun Sashe na 2 a ƙarƙashin Atisayen FANSAR YAMMA a Shiyyar Arewa maso Yamma, sun yi nasarar daƙile wasu hare-hare na yunƙurin garkuwa a Jihar Zamfara, inda suka ceto Shugaban makarantar Federal Polytechnic da ke Ƙauran Namoda, Dakta Aminu Yusuf, iyalansa da wasu fararen hula guda 21 a atisaye daban-daban. Rundunar soji ta sanar da cewa an gudanar da atisayen ne a ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, 2026, wanda ke nuna samun galaba da take yi a yaƙinta da ayyukan ta'addanci a sassan shiyyar. A wata sanarwa da Jami'in yaɗa labaran FANSAR YAMMA,…
Read More

Hukumar bogi: Shugabar Ma’aikata ta je gaban kwamitin majalisa yayin da Sufeto-Janar ya gaza kai Adeyemi kan hukuncin kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai da ke gudanar da bincike akan zargin hukumar kula da inganta zuba jarin ƙasashen waje ta shugaban ƙasa (PFIPC) ya sanar da takardar ɗaukar aiki ta wanda ya kira kansa da darakta janar ɗinta, Mista Adeniyi Adeyemi, a matsayin ta bogi duk da cewa Rundunar 'Yan sandan Nijeriya ba ta gabatar da shi ba a gaban kwamitin kamar yadda ya umarta. Akan haka ne wakilan 'yan sanda suka shaida wa kwamitin cewa suna buƙatar rubutaccen umarni daga kotu da zai ba su izinin fitar da Adeyemi…
Read More

Shugaban sojoji ya amince da naɗin jagororin sabbin bataliyoyin da Tinubu ya kafa

Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki wani sabon mataki na ƙarfafa tsarin aikinta, bayan Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu ya amince da nadin sabbin Shugabannin Runduna (General Officers Commanding - GOCs) domin jagorantar sabbin rundunoni hudu da aka kafa. Wannan sauyi ya biyo bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na faɗaɗa tsarin rundunar sojin ƙasar daga runduna takwas zuwa runduna 12, tare da shirin ɗaukar sabbin jami’an soja 28,000 domin ƙara ƙarfin rundunar. Sabbin naɗe-naɗen na daga cikin shirye-shiryen sake fasalin rundunar, inda aka kuma yi sauye-sauyen mukamai ga wasu manyan jami’an soja, ciki har da Brigadier…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka babban soja a yunƙurin garkuwa a Nasarawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin wasu 'yan bindiga suka halaka wani babban jami'in soja mai suna Kanal Abdussalam A. Ude yayin wani yunƙuri na kai harin yin garkuwa a yankin Badna da ke Ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya faru ne a yankin New Karu da ke iyaka da Birnin Tarayya Abuja, wanda da fari aka yi zaton ya faru ne a wani sashe na Abuja, kana daga bisani hukumomin tsaro suka tabbatar da cewa ya auku ne a Jihar Nasarawa. A cewar rahotanni, maharan sun je gidan jami'in ne…
Read More

Ɗangote ya rubuta wasiccin kaso uku na duniyarsa ga asusun taimako, inji ‘yarsa

Attajirin Nijeriya kuma shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote na shirin sadaukar da wani kaso mai yawa na dukiyarsa domin tallafa wa ayyukan jin ƙai, inda ɗiyarsa Halima Ɗangote, ta bayyana cewa mahaifin nata na da niyyar ware kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa domin taimakon jama’a. Halima ta bayyana cewa, wannan shiri wani ɓangare ne na burin mahaifinta na amfani da dukiyarsa wajen samar da sauƙi da inganta rayuwar al’umma, musamman ta fannonin lafiya, ilimi da rage ƙalubalen talauci. Dangote, wanda ke cikin jerin attajiran da suka fi kowa arziki a duniya, na da dukiyar da aka kiyasta…
Read More

Ɓarayi sun yi wa ɗalibai mata fashi a gidan kwanansu na Jami’ar ATBU

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu 'yan fashi sun kai farmaki a Jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBU) na yankin Gubi da ke Bauchi a tsakar daren wayewar ranar Litinin, inda suka ƙwace wa ɗalibai wayoyi da wasu kayayyaki masu daraja. Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kutsa cikin gidan kwanan ɗalibai mata ne da misalin ƙarfe 2 na daren ɗauke da adduna da wuƙaƙe, inda suka riƙa shiga ɗakuna suna yi wa ɗalibai fashi. Wata shaida da ta nemi a sakaye sunanta, ta ce maharan sun shiga sama da ɗakuna 10 a gidan tare da tserewa da sama da…
Read More

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam'iyyar adawa ta ADC da wasu jam'iyyu huɗu bisa rashin cika wasu sharuɗɗan shiga zaɓe. Kotun, a hukuncin da alƙalai uku suka yanke, ta ce babbar kotun ba ta da hurumin sauraron shari'ar, saboda ƙarar da aka shigar ba ta cika ka'idojin doka ba. Haka kuma, ta bayyana cewa babu ingantacciyar ƙara da za ta bayar da damar umarnin cire rajistar jam'iyyun a dokance. Kotun ta ce alkalin babbar kotun ya yi watsi da hujjojin da suka…
Read More

Tinubu ya umarci dakarun tsaro su farauto masu hannu a harin ƙauyen Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunonin soji da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta ƙaddamar da atisayen farauto waɗanda suke da hannu a mummunan harin da aka kai wa al'ummar ƙauyen Naridon da ke Gundumar Kamaru a Ƙaramar Hukumar Kaurun Jihar Kaduna. Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata takarda, ranar Talata. "In mai umartar sojoji, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ƙaddamar da atisaye a yankunan da abin ya shafa domin kama waɗanda suke da hannu da kuma dawo da doka da oda a shiyyar,"…
Read More

2027: Uba Sani ya ɗauki Jerry Adams a matsayin abokin tafiyarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya amince da ɗaukar Jerry Adams, wato Shugaban Hukumar Tattara Harajin jihar (KADIRS) a matsayin abokin tafiyarsa a zaɓen gwamnan 2027. A wani rubutu da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari da addu'o'i, lamarin da ke nuna fita daga tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a 2019 da 2023. A cewarsa, zaɓin ya nuna yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin ganin an kiyaye tsarin damawa da kowane ɓangare, gaskiya da adalci da kuma daidaito yayin gudanar da lamuran…
Read More