Babaji

5684 Posts

Kaduna: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 30 yayin da ‘yan bindiga suka farmaki ƙauye

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane 30 ciki har da yara takwas, aka halaka bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Naridon da ke Gundumar Kamaru a Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afka wa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren Lahadi wayewar Litinin, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da ƙauƙautawa ba, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama. Haka kuma, maharan sun cinna wa gidaje da dama wuta, wanda hakan ya jefa mazauna ƙauyen cikin firgici tare da tilasta wa wasu tserewa domin tsira da…
Read More

Majalisar Wakilai ta gayyaci Akanta Janar na Ƙasa, Ogunjimi kan badaƙalar hukumar bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Akanta Janar na Ƙasa (AGF), Shamseldeen Ogunjimi zai gurfana a gaban kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai a yau Litinin domin amsa wasu tambayoyi akan badaƙalar hukumar bogi da ake kira da Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC). Ogunjimi zai bayar ba'asi ne akan abin da ya sani game da yadda aka ware mata fiye da Naira biliyan 1.32 a cikin Kasafin Kuɗin shekarar 2026 duk da cewa babu ita. Kwamitin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kanke/Kanam/Pankshin ta Jihar Filato, Yusuf Gagdi ke jagoranta, na gudanar da bincike ne akan yadda aka kafa PFIPC,…
Read More

Abin da ya sa Buhari bai tallata Tinubu ba a fili gabanin zaɓen fidda gwanin APC – Babachir Lawal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana cewa marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu a filli a zaɓen 2023 ne saboda dalilan addini da lamuran ƙwarewa. Babachir Lawal ya faɗi haka ne a wata hira da gidan talabijin na Symfoni a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa da fari Buhari na ganin ba zai iya mara wa Tinubu baya ba a matsayin wanda zai gaje shi bisa la'akari da matsalolin lamuran addini da ƙwarewar siyasa. A cewarsa, bayan tattaunawa da tsohon shugaban, Buhari ya amince…
Read More

Tinubu ya karɓi Sanata Hanga da Sanata Gaya yayin da suka koma APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Lahadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin Maitaimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanatan Barau Jibrin, Sanata Rufa'i Hanga da kuma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Shugaban ya gana da manyan 'yan siyasar ne yayin shirin tarbar Sanata Hanga da Sanata Kabir Gaya wajen komawa cikin jam'iyyar APC, lamarin da ke nuna ƙarin ƙarfi ga jam'iyyar mai mulki yayin tunkarar zaɓen 2027. A yayin ganawar, Tinubu ya yi maraba da sanatoci biyun zuwa cikin APC, inda ya kuma jinjina wa matakin nasu na haɗewa da jam'iyyar domin…
Read More

An kama sojan da ake nema kan sayarwa ‘yan ta’adda kayan sojoji yana ƙoƙarin tafiya Kamaru

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar kama jami'i Private Mohammed Yusuf, wanda a kwanan nan aka sanar ana neman sa ruwa a jallo bisa zargin sayar kayan inifom ɗin sojoji da wasu kayayyakinsu ga 'yan ta'adda da sauran masu aikata miyagun laifuka. Rahotanni sun bayyana cewa, an kama Yusuf ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Asabar a matsayar motoci ta Jidar da ke Maiduguri a Jihar Borno, yayin da yake ƙoƙarin tafiya Jamhuriyar Kamaru. Jami'in yaɗa labarai na sojojin Atisayen Haɗin Kai (OPHK) na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni ne ya tabbatar…
Read More

An yi garkuwa da babban alƙali a Jihar Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi An wayi garin Lahadi cike da ruɗani a garin Bunza da kuma Jihar Kebbi bayan da waɗansu mutane suka yi garkuwa da ɗaya daga cikin manyan Joji-jojin jihar Kebbi Honarabul Yakubu Hassan Bunza a gidan sa da ke garin Bunza. Malam Ahmed Abdullahi Bunza wani makusancin Jojin ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja ta wayar tarho da cewa jiya da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare ne bayan ya dawo daga Sokoto ne waɗansu mutane kan babura biyar ɗauke da makamai suka tarye shi a ƙofar gidan sa da ke kan hanyar Zogirma suka…
Read More

Tinubu ya buƙaci likitoci da malaman asibiti da ke ƙasashen waje su dawo Nijeriya don bunƙasa fannin lafiya

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga likitoci da sauran ƙwararrun ma'aikatan lafiya na Nij reriya da ke zaune a ƙasashen waje su dawo gida domin ba da gudunmawa wajen bunƙasa harkokin lafiya da ci gaban ƙasa. Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Likitocin Najeriya mazauna ƙasashen waje, ƙarƙashin jagorancin babbar daraktar hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Shugaban ƙasar ya ce shi ma ya taɓa karatu da aiki a Amurka kafin ya dawo Najeriya, yana mai jaddada cewa "babu inda…
Read More

Matawalle ya umarci sojoji su ƙara ƙaimi bayan munanan hare-haren ‘yan ta’adda a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana ta'aziyya ga wadanda hare-haren ta'addanci ya shafa a Karamar Hukumar Bungudu da sauran al'ummomi a Jihar Zamfara. Haka kuma ya ba da umarnin a kara zafafa ayyukan soja a fadin yankin Arewa maso Yamma. A cikin wata sanarwa da mataimakin sa na musamman kan harkokin yada labarai, Ahmed Dan Wudil, ya fitar ranar Lahadi, Dr. Matawalle ya ce Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen mayar da zaman lafiya da tsaro duk da karuwar hare-hare da aka samu a wasu sassan Arewa maso Yamma. Ministan…
Read More

Jami’in kuɗin ISWAP ya miƙa wuya ga sojoji a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta yi gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da ayyukan tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas, bayan da wani babban jami'in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP tare da wasu yara maza guda biyu suka miƙa wuya ga dakarun Atisayen Haɗin Kai a Jihar Borno. Rundunar sojin ta sanar da haka ne a wata takarda a ranar Asabar, inda ta bayyana cewa an samun babbar nasara a yaƙin da take yi da ta'addanci da kuma amfani da bayanan sirri wajen daƙile harkokin 'yan ta'adda a Arewa maso Gabas. Jami'in…
Read More

Abin da ya faɗa ba gaskiya ba ne – Al-Mustapha bisa kalaman tsohon ɗan DSS kan mutuwar Abacha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Babban Hafsan Tsaron Shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustaph (mai ritaya), ya yi watsi da kalaman wani tsohon jami'in Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) akan lokutan ƙarshe na marigayin shugaban. Al-Mustaph ya bayyana kalaman a matsayin ƙarya, inda ya kuma yi kira ga 'yan Nijeriya da su watsi da su. Tsohon babban hafsan ya faɗi haka ne a wata hira da manema labarai bayan taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku da aka gudanar Arewa House da ke Jihar Kaduna a ranar Asabar. Ya yi…
Read More