Babaji

5684 Posts

Shettima ya jagoranci gwamnoni shida zuwa masana’antar tufafin Jamhuriyar Benin don farfaɗo da na jihohin Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na sake farfaɗo da masana'antun samar da kayan tufafi a Nijeriya, gwamnoni guda shida sun ƙudiri aniyar yin koyi da tsarin masana'antu na Glo-Djigbe Industrial Zone (GDIZ) na Jamhuriyar Benin domin ƙarfafa fannin samarwa da bunƙasa masana'antu a jihohinsu. Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin sun ci wannan alwashi ne a Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagorance su wajen ziyarar sanya ido a masana'antar da ke Cotonou, wadda ta zama abin koyi wajen amfani da salonta na juya harkokin noma zuwa samar da ababen masana'antu masu yawa. Wannan ziyara ɓangare ne…
Read More

Gwamnan Kaduna ya ƙaddamar da rabon taki kyauta ga manoma 150,000

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙaddamar da shirin rabon takin noma kyauta na daminar shekarar 2026 ga manoma ƙanana 150,000 a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce zai ƙara bunƙasa harkar noma da tabbatar da wadatar abinci. An ƙaddamar da shirin ne a Dandalin Murtala Square da ke Kaduna, inda gwamnatin ta sanar da rabon manyan motoci 500 na takin zamani tare da faɗaɗa tallafin amfani da injinan noma domin sauƙaƙa ayyukan noma ga manoma. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa shirin na daga cikin manufofinta na ƙarfafa samar da abinci, rage tsadar noma da…
Read More

Ganduje ya gana da Sanata Kabiru Gaya kwanaki bayan shugaban APC ya ziyarce shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar girmamawa ta musamman ga tsohon gwamna kuma tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya a gidansa da ke Abuja. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya kai wa Sanata Kabiru Gaya, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin cigaba da tattaunawa, haɗin kai da ƙarfafa zumunci tsakanin manyan jagororin jam'iyyar. Ana ganin wannan a matsayin tayi na masamman domin janyo ra'ayin tsohon sanatan ya sauya sheƙa zuwa…
Read More

Jonathan da Osinbajo sun ziyarci mayaƙan Neja-Delta, wa zai je wajen Boko Haram? – Sheikh Gumi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ƙalubalanci dalilin da ya sa babu wani jami'in gwamnati da ya taɓa ziyartar jagorancin ƙungiyar Boko Haram da 'yan bindiga a hukumance domin tattaunawa akan kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a sassan Nijeriya, yana mai cewa jagororin gwamnatoci a baya sun yi amfani irin salon wajen warware matsalolin rikicin 'yan yankin Neja-Delta. Sheikh Gumi ya bayyana haka ne a wani rubutu da aka ɗauko daga shafinsa na Facebook a ranar Asabar, inda ya kamanta salon gwamnatin da al'amarin rashin tsaro na Arewa, yana mai cewa tsohon shugaban…
Read More

Ƙuri’un ‘yan ƙasa za su yi hukunci a zaɓen 2027, inji Amupitan ga Abdulsalam

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Joash Amupitan, ya bayyana cewa ƙuri’un ‘yan Nijeriya za su kasance masu daraja kuma za a tabbatar da sun yi tasiri a babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027. Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ziyarar girmamawa da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a gidansa da ke Minna, babban birnin Jihar Neja. A yayin ganawar, shugaban INEC ya bayyana Abdulsalami Abubakar a matsayin “uban dimokuraɗiyyar Najeriya”, yana mai yaba irin rawar da tsohon shugaban ƙasar ya taka wajen tabbatar da komawar mulki hannun farar hula a…
Read More

Matuƙar INEC ba ta dogara da kanta ba ta fuskar kuɗi ba za ta ci gashin kanta ba, inji Amupitan

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ba za ta iya gudanar da aikinta cikin cikakken ‘yanci ba muddin ba ta da cikakken ikon cin gashin kai ta fuskar harkokin kuɗi. Amupitan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro, inda ya jaddada cewa samun ‘yancin kuɗi na daga cikin muhimman sharuɗɗan da za su tabbatar da cikakken ‘yancin hukumar wajen gudanar da zaɓe ba tare da wani tasiri daga waje ba. Ya bayyana cewa duk da cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadi zaman kansa ga INEC, har yanzu akwai buƙatar…
Read More

Shugaban ƙasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Mohammed Shahabuddin na ƙasar Bangladesh mai shekaru 76 ya sanar da yin murabus daga muƙamin shugabancin ƙasar, inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda matsalolin da suka shafi lafiyarsa. Murabus ɗin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsin lamba na siyasa. Ficewarsa ta kawo ƙarshen kasancewar babban jigon gwamnati na ƙarshe da ke da alaƙa da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina, wadda aka hambarar daga mulki. A halin yanzu, rahotanni na nuna cewa Sheikh Hasina na shirin dawowa daga gudun hijira, lamarin da ka iya sake tayar da…
Read More

DSS ta kama jagoran matasan Borno kan zargin da ya yi na an biya Boko Haram fansar biliyan N5

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta kama Shugaban Ƙungiyar Matasan Borno ta Kudu (BOSYA), Samaila Ibrahim Kaigama bayan wasu kalamai da ya yi a hirar talabijin, inda ya yi zargin cewa an biya mayaƙan Boko Haram da 'yan bindiga kuɗaɗen fansa. Rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Kaigama zuwa ofishin DSS ne jim-kaɗan bayan kammala hirar, wadda aka gudanar da ita a tashar Channels, inda ya yi tsokaci akan ƙalubalen da arewacin Nijeriya ke fuskanta kuma ya yi iƙirari akan batun sako mutanen da aka sace a Borno. A yayin hirar, Kaigama…
Read More

‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da kashe jami’an tsaro a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne, sun yi awon-gaba da Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Bunguɗu, bayan ƙaddamar wani mummunan hari da dare a gidansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro guda uku. An ruwaito cewa maharan sun kai farmakin ne acikin daren Alhamis wayewar Juma'a, inda suka farmaki gidan ciyaman ɗin da ke yankin Zango, ƙasa da kilomita 20 daga Gusau, Babban Birnin jihar. A yayin harin, 'yan bindigar sun nuna fin ƙarfi ga jami'an da ke gadin gidan, inda suka halaka 'yan sanda da 'yan…
Read More

Mun ɗauka rasuwa za mu yi, inji ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin Enugu Air da suka tsira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani fasinjan jirgin Enugu Air da ya yi saukar gaggawa a filin jiragen saman Benin, ya bayyana yadda suka tsinci kansu a cikin halin firgici yayin da jirgin nasu ya goce daga ainihin titinsa. Ya yi zargin cewa jami’an gudanarwa sun gaza kula da al'amarin, inda ya ce har yanzu kamfanin bai bayar da haƙuri a gare su ba a hukumance. Fasinjan, wanda sanannen na siyasa ne a Jihar Edo, ya magantu ne bisa neman a sakaye sunansa, ya bayyana cewa, jirgin ya taso ne daga filin Murtala Mohammed sashe na 2 (MM2) da…
Read More