Babaji

5684 Posts

Ɗaya daga cikinmu ba ya iya biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansa, inji ɗan Majalisar Wakilai kan zargin biyan su sama da kima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɗan Majalisar Wakilai mai suna Chunedu Obika, ya ƙalubalanci batun da ake yaɗawa cewa ana biyan 'yan majalisar dokokin ƙasa sama da kima, yana mai cewa kwanan nan ya samu labarin cewa ɗaya daga cikin takwarorinsu ya fuskanci ƙalubale wajen samar da kuɗin karatun 'yarsa Naira 700,000. Obika, wanda ke wakiltar AMAC/Bwari a Majalisar, ya ce shi ne wanda ya tallafa wa ɗan majalisar biyan kuɗin makarantar kimanin wasannin biyu da suka gabata. Ya bayyana haka ne yayin wata hira da KAA Truths da aka wallafa a ranar Alhamis yayin amsa tambaya akan…
Read More

Gwamnatin Zamfara ta jajenta wa ƙauyen da aka halaka wa manoma 23

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta aike da gaisuwar ta'aziyyarta ga al'ummar ƙauyen Sauna da ke Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara, bayan wani mummunan harin 'yan bindiga da ya yi sanadiyyar ajalin mutane 26 da raunata wasu guda huɗu. Maitaimakin gwamnan jihar, Alhaji Mani Malam Mummuni Masamar Mudi ne ya kai gaisuwar a madadin gwamnatin jihar ga al'ummar ƙauyen a ranar Juma'a. Da yake jawabi, Mummini Masamar ya jaddada aniyar gwamnatinsu ta ƙoƙarin kawo ƙarshen ayyukan 'yan bindiga a faɗin jihar. Ya ce, gwamnatin Zamfara ba ta taɓa yin wata tattaunawar sulhu da 'yan bindiga ba, yana…
Read More

Obasanjo da Atiku sun fara tada jijiyar wuya kan zarge-zargen makircin tsigewa da wa’adi na uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar, sun sabunta tsohon rikicin su na siyasa, yayin da suka fara musayar zarge-zarge akan zargin kitsa tsigewa da shirin neman wa'adi na uku da suka sanya dangantakarsu ta yi tsami. Obasanjo ya zargi Atiku da ba wa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba Naira miliyan 5 domin ya fara tsara shirin tsige shi tun a wa'adinsa na farko a matsayin shugaban ƙasa. Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan zargi ne a lokacin da yake bayar da amsa game da kalaman tsohon…
Read More

Ya dace ‘yan adawa su riƙa ƙarfafa gwiwa ga ƙoƙarin Tinubu da Trump na kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya, inji Iliyasu Kwankwaso

Ƙoƙarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi na samar da tsaro a ko'ina cikin fadin Najeriya nata jan hankalin al'ummar duniya. Kwanan nan ne Mista Donald Trump, Shugaban Kasar Amurka, ya jinjina wa Shugaba Tinubu kan nasarorin da yake samu wajen wanzar da zaman lafiya a Najeriya. Wannan alamar ce ga yan adawa su daina sukar gwamnati, su taho su hada hannu wajen samar da cikakken tsaro a fadin Nijeriya. Wannan shine sakon Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso, Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are, wanda ya sanya hannu aka rabawa yan jarida. Musa…
Read More

An zargi ‘yan sandan Afirka ta Kudu da lakaɗa wa ɗan Nijeriya duka har lahira a Cape Town

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An zargin wasu jami'an hukumar 'yan sandan ƙasar Afirka ta Kudu (SAPS) da halaka wani ɗan Nijeriya mai suna Mista Chika Ibe a lokacin da suke gudanar da atisaye a yankin Parksig Villas da ke Belleville a Birnin Cape Town. Rahotanni sun bayyana cewa, Ƙungiyar 'yan Nijeriya mazauna ƙasar (NICASA) ce ta bayyana haka, inda ta yi alla-wadai da mummunan kisan ɗan Nijeriyar, inda ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike akan al'amarin. A cewar NICASA, Mista Ibe, wanda ɗan yankin Lokpaukwu na Jihar Abia ne, ya haɗu da ajalin nasa ne…
Read More

Jaddawali: Lauyoyi 68 da aka ƙara wa matsayi zuwa SAN

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Walwalar Masana Shari'a ta Ƙasa, ta amince da ƙarin matsayi ga wasu lauyoyi guda 68 zuwa matsayin babban lauyan Nijeriya (SAN). An ɗauki wannan mataki ne a zaman kwamitin karo na 174 da aka gudanar a ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2026, ƙarƙashin jagorancin Alƙalin alƙalan Nijeriya, Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun. Waɗanda suka yi nasarar kai wa matsayin sun haɗa da lauyoyi 67 da wani farfesa da ke karantarwa a babbar makaranta mai suna Nnamdi Obiareri. Haka kuma, acikinsu akwai tsohon kakakin Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Habeeb Lawal da tsohon shugaban NBA na…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki Atiku kan ɗaukar nauyin kamfanin Amurke don adawa da mulkin Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, bayan zarginsa da ɗaukar hayar masu fafutukar siyasa a Amurka kan kuɗi dala miliyan 1.2 domin kai ƙorafi ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan wata shari’ar ƙwace kadarori ta shekarar 1993 da ta shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana matakin da ake zargin Atiku ya ɗauka a matsayin yunƙurin…
Read More

Gwamnan Nasarawa ya tsige kwamishinoni

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi wani ƙaramin garambawul ga tawagar manyan jami'an gwamnatinsa. Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Shuaibu Labaran Magaji ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwar gwamnatin a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2026 a Lafia. A cewarsa, gwamnan ya ce sauye-sauyen wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa shirye-shiryen gwamnatin na tunkarar babban zaɓen 2027 da ke cigaba da ƙaratowa. Ya sanar da cewa, kwamishinoni guda shida ne aka sauke daga muƙaminsu, waɗanda suka haɗa da kwamishinan lamuran tsaro, Usman Baba, kwamishinan filaye, David Moyi, kwamishinar harkokin mata…
Read More

Tinubu ya amince da faɗaɗa shiyyoyi zuwa 12 da ɗaukar jami’ai 28,000 a rundunar soji

Shugaba Bola Tinubu ya amince da faɗaɗa tsarin Rundunar Sojin Nijeriya daga rundunoni takwas zuwa 12 tare da ɗaukar sabbin sojoji 28,000 domin ƙarfafa tsaron ƙasa. Sanarwar da Kakakinsa Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce matakin zai inganta jagoranci da gudanar da ayyukan soja, ƙarfafa tsaron kan iyakoki, kare muhimman ababen more rayuwa, da kuma haɓaka yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro. Sabbin rundunonin za su kasance a Makurɗi, Ilorin, Jalingo da Benin City, yayin da za a aiwatar da sabon tsarin kashi biyu. Kashi na farko zai kammala nan da watan Satumban 2026, yayin da…
Read More

Rundunar soji na neman wani jami’i ruwa a jallo kan samar wa ‘yan ta’adda kayan sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Dakarun Sojojin Nijeriya sashen jami'an Ordnance Corps (NAOC), ta sanar da neman ɗaya daga cikin jami'anta ruwa a jallo kan zargin sa da hannu a sayarwa da samar da kakin sojoji ga 'yan ta'adda da wasu masu aikata miyagun laifuka. Bincike ya nuna cewa, sojan, wanda yake aiki a sashen masana'antar haɗa kayan sojoji, ya bar wajen aikinsa ne tun a ranar 3 ga watan Yuni, 2026 domin guje wa kamu. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na sojoji, Manjo Oluwatope Aluko ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an ayyana…
Read More