Babaji

5684 Posts

Matatar Ɗangote ta koma sayar da fetur a naira daga dala, ta yi ƙarin N140

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matatar Man Fetur ta Ɗangote ta koma sayar da fetur da kuɗin naira bayan dakatar da tsarin amfani da dala yayin da ta kuma yi ƙarin N140 daga yadda ta saba sayarwa a defo. Hakan na zuwa ne bayan da matatar, mai samar da gangar mai 650,000 a kullum, ta dakatar da dakon fetur da koma wa amfani da dala wajen tsara farashi, lamarin da ya janyo tsaiko a harkar samarwa da kasuwar fetur da ya sa aka samu ƙarin farashi a defo. Matatar ta yi wannan sanarwa ne a wani saƙon da ta…
Read More

DSS ta ceto sauran ɗaliban Polytechnic huɗu da aka sace a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS a Jihar Zamfara, ta yi nasarar ceto sauran ɗalibai guda huɗu da aka yi garkuwa da su Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, 'yan makarantar 'Federal Polytechnic' da ke ƙaramar hukumar. Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an sun samu wannan nasara ne bayan amfani da wasu bayanai na sirri, lamarin da ya ba su damar ceto ɗaliban da suka haɗa da maza uku da mace guda a ranar Laraba ba tare da biyan kuɗin fansa ba. Haia kuma, an ruwaito cewa an kama ɗaya daga cikin masu garkuwar a lokacin atisayen…
Read More

Ɗan shekara 60 ya rasu a otel yayin da ya je da ‘yar shekara 20 a Jigawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Jigawa, ta ce ta fara gudanar da bincike akan mutuwar wani tsohon ɗan kimanin shekaru 60 da ya rasu bayan shiga halin kulawar gaggawa a wani ɗakin otel da ke Dutse, babban birnin jihar. Al'amarin ya auku ne a ranar Talata, 21 ga Yuli, 2026, yayin da ya je otel ɗin da wata mata mai shekaru 20. A wata sanarwa da jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce marigayin ya shiga otal ɗin tare da wata mata mai shekara 20. A cewarsa,…
Read More

Gwamnan Zamfara ya amince da ƙudirin gyaran dokokin ilimi da gudanar makarantu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan wasu Dokokin Zartarwa da za su kafa sabon tsarin gudanar da harkokin ilimi a jihar, tare da ƙaddamar da rabon Manhajar Karatu ta Ƙasa ga makarantun gwamnati. Gwamnan ya ƙaddamar da shirin ne a ranar Talata yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau. A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa dokokin zartarwar sun ƙunshi sabbin tsare-tsaren gudanar da harkokin kuɗaɗen ilimi, kare makarantu, tantance…
Read More

Tinubu ya kafa sabuwar bataliyar sojoji a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ƙoƙarinsa na ƙarfafa tsaro da yaƙi da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a Jihar Kwara. A sanarwar da Mataimakin Sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kwara, Mashood Agboola ya fitar, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce za a kafa bataliyar ne a garin Omu Aran, wato hedikwatar Ƙaramar Hukumar Irepodun. Gwamna AbdulRazaq ya yaba wa Tinubu bisa amincewa da bukatar, yana mai cewa sabon sansanin sojojin zai kara karfin ayyukan yaki da ta'addanci da masu garkuwa da mutane a jihar.…
Read More

Ministan Tsaro ya musanta jita-jitar murabus yayin da ya gana da Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ci alwashin ɗaukar matakin shari'a akan waɗanda suke yaɗa rahotannin da ke zargin cewa ya yi murabus daga muƙaminsa, inda ya ce hakan ya matuƙar girgiza shi kuma bai san daga ina aka samo zancen ba. Janar Musa ya bayyana haka ne jim-kaɗan bayan wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ministan ya isa fadar ne da misalin ƙarfe 3 na yamma kuma ya tafi bayan sa'a guda yayin da ake raɗe-raɗin makomarsa a kujerar muƙamin…
Read More

2027: Tikitin NDC na Obi da Kwankwaso ba zai yi nasara ba a Kano, inji Ganduje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa da ya haɗa Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso a jam'iyyar NDC ba zai yi nasara ba a Jihar Kano a babban zaɓen 2027. Ganduje, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya faɗi haka ne yayin ganawa da 'yan jarida a ranar Talata, inda ya ce tikitin takarar ba shi da ƙarfi a siyasance, karɓuwa ko kuma tarihin shugabanci da ake buƙata domin samun goyon bayan al'umma a jihar. "Ba na tunanin tikitin Peter Obi da Kwankwaso zai yi nasara…
Read More

Majalisar Dattawa ta gayyaci Ribaɗu da ministan harkokin waje kan badaƙalar hukumar bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙwarya-ƙwaryar kwamitin Majalisar Wakilai kan binciken badaƙalar hukumar bogi ta PFIPC, ya koka kan yadda jagororin wasu ma'aikatu da hukumomi suka ƙi amsa gayyatarsa akan al'amarin. A ranar Talata bayan kammala zaman majalisar ne shugabancin kwamitin ya bayyana wannan koke, inda ya ce rashin amsa gayyatar tasu na haifar da koma-baya ga aikin binciken da suke gudanarwa da kuma matakin shari'a akan hukumar. Haka kuma, kwamitin ya soki rashin ganin Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, wanda wani jami'in ma'aikatar ya wakilce shi, yana mai cewa wajibi ne su amsa gayyatar kai-tsaye na zuwa da kansu…
Read More

‘Yan sanda ke kan gaba yayin da ICPC ta fallasa ma’aikatan bogi 908 da ƙwato zambar miliyan N942

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta gano cewa akwai ma'aikatan bogi da dama a Rundunar 'Yan Sanda ta Nijeriya da ma’aikatun gwamnati guda biyar da hukumomin tarayya yayin da take nazari akan albashin ma’aikata. Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN) ne ya bayyana haka yayin da yake magana kan binciken damfara a cikin biyan albashi a hukumomin gwamnatin tarayya. Hukumar ta ce ta gano ma’aikata 'yan jabu guda 908 a ma’aikatun gwamnati, sassa da hukumomi aƙalla 50. Haka kuma, ta dawo da kimanin Naira miliyan 942 da ake zargin an biya…
Read More

NNPC ya ƙara farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya ƙara farashin litar man fetur a gidajen sayar da man da ke ƙarƙashin ikonsa. Rahotanni sun nuna cewa kamfanin ya ɗaga farashin daga N1,155 zuwa N1,270 kan kowace lita a Abuja da kewaye, wanda ke nuna ƙarin Naira 115. Rahotanni sun ce wasu gidajen mai na NNPCL da MRS sun dakatar da sayar da fetur na ɗan lokaci, yayin da sauran gidajen mai suka ƙara farashin sakamakon sauye-sauyen da ke faruwa a kasuwar man fetur. Karin farashin ya zo ne bayan masu gidajen ajiya da dillalan…
Read More