Babaji

5684 Posts

Shugaban La Liga na neman Infantino ya yi murabus kan zargin rashin adalci a gasar Kofin Duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban gasar La Ligar ƙasar Sifaniya, Javier Tebas, ya buƙaci Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino da ya gaggauta yin murabus daga muƙaminsa kan abin da ya kira da "ɗaukar matakai masu haifar da cece-kuce" da ke rusa harkar ƙwallon ƙafa. A wata hira da jaridar ƙasar Italiya La Gazzetta dello Sport, Tebas ya zayyano matsaloli da dama ciki har da hutun shan ruwa, ƙarin lokacin hutun rabin lokaci da ya ba taurarin waƙa damar gabatar da wasa, shiga tsakani kan dakatar da ɗan wasa da kuma buƙatar neman a ƙara…
Read More

Zidane ya maye gurbin Deschamps a matsayin kocin Faransa bayan rattaɓa hannu a doguwar kwantaragi

Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Faransa, Zinedine Zidane, ya rattaba hannu kan yarjejeniya da za ta ba shi damar zama sabon kocin tawagar ƙasar Faransa har zuwa watan Yunin 2030, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Kwararren ɗan jaridar kasuwar musayar 'yan wasa, Fabrizio Romano, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce za a gabatar da Zidane a hukumance cikin kwanaki masu zuwa. Rahoton ya ce Zidane zai jagoranci Faransa a gasar UEFA Nations League ta 2027, Gasar Kofin Nahiyar Turai (Euro 2028), da kuma Gasar Cin Kofin Duniya ta 2030. Zidane mai shekaru 54…
Read More

2027: Shugaban APC na Ƙasa ya sake ganawa da Sanata Kabiru Gaya

Tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya ganawar sirri da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a gidansa da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa, ganawar ta ɗauki kusan mintina 45, inda aka tattauna kan batutuwan siyasa da kuma makomar jam'iyyar APC a Jihar Kano. Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa Sanata Gaya ya nuna aniyarsa ta komawa jam'iyyar APC, duk da cewa har yanzu babu wata sanarwa daga gare shi da ta tabbatar da hakan a hukumance. A nasa ɓangaren, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tabbatar da cewa ya karɓi baƙuncin…
Read More

NIHSA ta gargaɗi Kano, Adamawa, Jigawa da wasu jihohi 14 kan yiwuwar ambaliya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Ƙasa (NIHSA), ta fitar da sanarwar gargaɗi na kwana bakwai akan yiwuwar aukuwar ambaliya a jihohi guda 17 na sassan Nijeriya daga ranar 21 zuwa 27 ga watan Yuli, 2026. Darakta-Janar na NIHSA, Umar Mohammed, ya ce an ɗauki matakin ne bayan hauhawar matakan ruwa a wasu manyan koguna, lamarin da ka iya haddasa ambaliya a wasu yankuna. Umar Mohammed ya ce, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Benuwai, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Nasarawa, Neja, Filato, Taraba, Yobe da kuma…
Read More

Gwamnan Jigawa ya samu ofisoshi babu manyan jami’ai yayin da ya kai ziyara a sakatariya ranar aiki

A ranar Litinin Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kai wata ziyara ta ba-zata a sakatariyar gwamnatin jihar domin duba yadda ma'aikata ke gudanar da ayyukansu, inda ya samu mafi yawancin ma'aikata ba su halarta ba. A yayin ziyarar, gwamnan ya tarar da ofisoshin manyan jami'an sakatariyar da dama a kulle, yayin da kuma ya gano cewa da yawa daga cikin manyan ma'aikata ba su halarci wuraren ayyukansu ba, duk da cewa lokacin ya kai ziyarar kusan ƙarfe 11:00 na safe ne. A cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Namadi yana…
Read More

2027: Kwankwaso ya tabbatar da yarjejeniyar wa’adi guda da Obi a rubuce

A ranar Litinin Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Rabi'u Kwankwaso, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyarsu a zaɓen 2027, Peter Obi, ya amince a rubuce da yarjejeniyar tsarin shugabancin Nijeriya na wa'adin shekaru huɗu kacal. Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata hira da shi a gidan talabijin na Channels. Rahotanni sun bayyana cewa yarjejeniyar ta tanadi cewa Peter Obi zai yi wa’adi guda ɗaya kacal na shekaru huɗu a matsayin shugaban ƙasa, kafin mulki ya koma yankin Arewa domin cigaba da tsarin daidaito da raba madafun iko tsakanin…
Read More

Jigawa: Sama da mata da yara 40 sun rasu yayin kifewar kwale-kwale a Ringim

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani mummunan hatsarin kwale-kwale ya auku a yankin Malamawa ta ’Yan Dutse da ke Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa, inda mata da yara Sama da 40 suka nutse a cikin ruwa. Bayanan farko sun nuna cewa mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da har yanzu jami’an ceto tare da mazauna yankin ke ci gaba da lalubo wasu fasinjojin da ba a gano inda suke ba. An kuma yi nasarar ceto wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa. Har zuwa wannan lokaci, ba a bayyana musabbabin kifewar kwale-kwalen ba, kuma hukumomin da abin ya…
Read More

DSS na neman a rataye jagororin Ansaru biyu bayan ƙin amince wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai akansu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta shirya ɗaukaka ƙara akan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa jagororin ƙungiyar ta'addanci ta Ansaru biyu a ranar Litinin, 20 ga Yuli, 2026. Mai Shari'a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne jim-kaɗan bayan da Mahmud Usman da ake kira Abu Bara’a ko Abbas ko kuma Mukhtar da Abubakar Abba da aka sani da Mahmud al-Nigeri/Malam Mamuda, wanda shi ne mataimaki kuma jagoran mayaƙa suka amsa hannu a laifuka guda 32 masu alaƙa da ta'addanci. Saidai, bayan kammala zaman hukuncin, wani babban jami'in DSS…
Read More

Majalisar Wakilai ta fara bincike yayin da CBN ya tabbatar da buɗe asusu ga hukumar bogi da amincewar AGF

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Bankin Nijeriya CBN, ya shaida wa ƙwarya-ƙwaryar kwamitin binciken shari'ar lamarin hukumar bogi ta PFIPC na Majalisar Wakilai cewa ya samu sahalewar ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) domin buɗe asusu guda biyu ga hukumar. Hakan na zuwa ne bayan da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) a ranar Litinin ta gayyaci Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila domin amsa wasu tambayoyi kan zarge-zargen da Shugaban Hukumar bogin, Adeyemi Adeniyi ya yi akansa game da al'amarin. Adeniyi ya yi zargin cewa ya ba wa Gbajabiamila Naira miliyan 400 ta hannun…
Read More

An yanke wa jagororin Ansaru biyu hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan gano suna da hannu a sace ‘yan Oyo

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wasu manyan jagororin ƙungiyar Ansaru biyu hukuncin daurin rai da rai bayan sun amsa laifukan ta'addanci 32 da hukumar DSS ta tuhume su da su. Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mahmud Usman (Abu Bara'a), wanda ake zargi da jagorantar Ansaru, da mataimakinsa Abubakar Abba (Malam Mamuda). Mai shari'a Emeka Nwite ya ce ya yi la'akari da roƙon da lauyansu ya gabatar kafin ya yanke hukuncin. Kotun ta yanke musu daurin rai da rai kan laifukan ɗaukar nauyin ta'addanci ta hanyar amfani da kuɗaɗen haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida…
Read More