20
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya bayyana a gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC ) don amsa wasu tambayoyi akan zargin sa da hannu a lamarin hukumar bogi ta PFIPC. Rahotanni sun bayyana cewa, Gbajabiamila ya amsa gayyatar ICPC ne a ranar Litinin, inda aka masa wasu tambayoyi a game da binciken da ake gudanarwa kan ayyukan PFIPC da aka bayyana a matsayin ta bogi. Lauyansa, Jiti Ogunye ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce shugaban ma'aikatan ya bayar da cikakken haɗin kai ga masu bincike…
