Babaji

5684 Posts

Sojoji sun kama ɗan bindigar da ya addabi hanyar Jos zuwa Makurɗi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun sashe na 6 da ke aiki a ƙarƙashin Atisayen Enduring Peace, sun yi nasarar kama wani da ake zargin ƙasurgumin ɗan dabar masu garkuwa da mutane ne da aka alaƙanta da wasu hare-hare da garkuwa akan babban titin Jos zuwa Makurɗi a Jihar Filato. Masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ne ya sanar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafin X a ranar Juma'a. A cewar rubutun, an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar 16 ga watan Yuli yayin wani atisaye da dakarun suka ƙaddamar…
Read More

Ta yiwu akwai wakilan ‘yan ta’adda cikin sojoji da ‘yan sanda, inji mai taimaka wa Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai ba wa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Daniel Bwala, ya bayyana cewa akwai wasu mutane da ke aiki a matsayin wakilan 'yan ta'adda acikin rundunonin soji da 'yan sanda a Nijeriya. Bwala ya faɗi haka ne yayin wata tattaunawa a shirin The Link Podcast a ranar Juma’a, a lokacin da yake amsa tambaya akan ko Rundunar Sojin Nijeriya na fama da matsalolin wakilan ayyukan ta'addanci. Ya tunatar da yadda a baya aka riƙa kama jami'an soji da na 'yan sanda bisa alaƙa da ayyukan ta'addanci a Nijeriya. Ya ce,…
Read More

Ƙungiyar YAN ta kafa kwamitin babban taronta na ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Taron Matasan Nijeriya (YAN), ya sanar da kafa kwamitin shirya babban taronta na ƙasa da za gudanar a nan gaba. A sanarwar da kwamitin amintattun ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an shirya kwamitin ne bisa la'akari da tabbatar da tsare gaskiya da adalci ga kowane ɓangaren ƙasa. Akan haka ne ma aka zaɓo wakilai daga baki ɗaya shiyyoyi guda shiga na faɗin Nijeriya, domin su tsara yadda za a gudanar da taron ba tare da fuskantar wata babbar matsala ba. Ga jaddawalin 'yan kwamitin kamar yadda sanarwar ta…
Read More

Sojoji sun daƙile harin ISWAP na sace ɗalibai da dama a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai (OPHK) tare da 'yan sandan MOPOL, sun yi nasarar daƙile wani babban harin garkuwa daga wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne a makarantar Kwalejin Tarayya ta Mata (FGGC) da ke Monguno a Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare a ranar Lahadi, 19 ga Yuli a makarantar, wadda a yanzu gwamnatin jihar ke amfani da ita a matsayin wajen kwanan ɗaliban Polytechnic ta Tarayya ta Monguno na wucin-gadi. Jami'in yaɗa labarai na OPHK, Kyaftin Mohammed Goni ne…
Read More

Shettima ya tafi Sierra Leone wakiltar Tinubu a taron ECOWAS na 69

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja, idna ya nufi zuwa Freetown, babban birnin ƙasar Sierra Leone domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Ƙungiyar Ƙasashe Masu ƙarfin Tattalin Arziƙi ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) karo na 69. Taron, wanda za a gudanar a ranar Asabar a babban ɗakin taro na Julius Maada Bio, Freetown, zai haɗa kan shugabannin ƙasashe, ministoci, manyan jami'an gwamnati da cibiyoyin shiyya domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi Afirka ta Yamma. A wata sanarwa da Kakakin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce Shettima zai…
Read More

Ingila ta samu kyauta cikin shekaru 60 a gasar Kofin Duniya bayan doke Faransa a wasan neman na uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Ingila ta kammala gasar Kofin Duniya na 2026 cikin nasara bayan doke Faransa da ci 6 da 4, inda ɗan wasa Bukayo Saka ya zura ƙwallo uku a wasan. Wannan ya nuna cewa, Ingila ta samu mafi kyan nasara a gasar acikin shekaru 60. Wasan, wanda aka buga a filin Miami a yammacin ranar Asabar, ya ɗauki hankalin 'yan kallo musamman ganin yadda Faransa ta yi ta ƙoƙarin farfaɗowa amma Ingilar ta ƙi ba ta dama, lamarin da ya sa wasan ya zama ɗaya daga cikin irinsa da aka fi zura ƙwallaye masu…
Read More

Burna Boy da Shakira za su yi waƙa yayin hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na Kofin Duniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen mawaƙin al'adun Afirka kuma ɗan Nijeriya, Burna Boy tare da shahararriyar mawaƙiyar nan ta ƙasar Kolombiya, Shakira, sun sake haɗuwa gabanin wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2026, inda za su nishaɗantar da masu kallo yayin da aka tafi hutun rabin lokaci a wasan. A wani bidiyo da Burna Boy ya wallafa a kafar X, an ga yadda mawaƙan duniyar biyu suke gaisawa cikin nishaɗi yayin da suke shirya wa gabatar da wasa a wasan ƙarshe na Kofin Duniyar. Mawaƙin, wanda ya taɓa lashe kyautar Grammy, ya bayyana farin cikinsa akan gabatar…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta faɗi yadda rashin jituwar sojoji a malkin Buhari ya haifar wa yaƙar ta’addanci tasgaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Daniel Bwala ya yi zargin cewa hamayya tsakanin Rundunar Soji da Rundunar Sojin Sama na Nijeriya a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari ya yi sanadiyyar hana wa dakarun tsaro tallafin jiragen sama na yaƙi a lokutan wasu atisaye. Bwala ya yi iƙirarin cewa rashin jituwa tsakanin ɓangarorin jagoranci biyun a lokacin ya taimaka wajen haddasa tsaiko da rashin samun amsa daga ɓangaren dakarun tsaro a duk lokacin da suka nemi agajin sama yayin wasu atisaye. Mai taimaka wa shugaban ya…
Read More

Gwamnati ta fara bincike yayin da wani yaro ya rasu sakamakon baƙuwar cuta a Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Neja ta ƙaddamar da bincike akan zargin ɓullar wata cuta bayan wasu rahotannin cewa wani rashin lafiya ya yi ajalin wani yaro da kuma shafar 'yan gidansu, inda aka yi kira ga al'umma da su kwantar da hankali da tabbatar da yi wa 'ya'yansu rigakafi akai-akai. Daraktan yaɗa labarai na Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Yunusa Sa'idu ne ya bayyana haka a wata takarda, inda ya ce gwamnatin ta yunƙura ne bayan mahaifin yaron ya yaɗa bidiyoyi a kafafen Soshiyal Mediya cewa wata cuta ta shiga cikin gidansa. Da yake…
Read More

Amaechi ya janye ƙara akan Atiku yayin da kotu ta yi watsi da ƙalubalantar zaɓen fidda gwanin ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi ya shigar na ƙalubalantar nasarar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC da aka gudanar a kwanakin baya. Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce ta yi hukuncin a ranar Juma'a bayan lauyan Amaechi, Jibrin Okutepa ya nemi kotun ta amince wa janye ƙarar daga ɓangarensu. Okutepa ya shaida wa kotun cewa, waɗanda al'amarin ƙorafin ya shafa sun warware saɓanin da ke tsakaninsu, wanda hakan ya sa aka ɗauki…
Read More