Babaji

5684 Posts

2027: Neman shiga takarar Jonathan ya samu tasgaro bayan kotu ta yi watsi da buƙatar tabbatar da shugabancin tsagin su Turaki a PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke neman tilasta wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta amince tare da bayyana sunayen Kwamitin riƙo na Jam'iyyar PDP, wanda Kabiru Turaki ke jagoranta da tsaginsu ya shigar a gabanta. Mai Shari'a Salim Ibrahim a yayin hukuncin, ya bayyana cewa masu shigar da ƙarar waɗanda Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ke jagorantar su, ba su da hurumin shigar da ƙarar. Akan haka ne kotun ta yi watsi da ita bisa rashin ikon sauraron ƙarar a dokance, lamarin da ya…
Read More

NiMet ta yi hasashen mamakon ruwan sama na kwana uku daga Asabar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama da hasken rana daga ranar Asabar zuwa Litinin a sassan Nijeriya. A takardar bayanin hasashen da ta fitar a ranar Juma'a a Abuja, NiMet ta ce rana za ta haska a yankin arewacin Nijeriya da kuma matsakaicin hadari. Hukumar ta yi hasashen samun tsawa da walƙiya da matsakaici ruwan sama a wasu sassan jihar Taraba a lokutan rana da kuma dare. Ta ce, za a samu yanayin hadari a Arewa ta Tsakiya a tsakanin ranakun a sassan ƙasar. A kudancin…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutum uku bisa zargin hannu a sace ɗalibai da malaman Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da wasu mutane uku bisa zargin su da hannu a garkuwa da ɗalibai da malaman makarantar Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo da aka ceto a kwanan nan. Mutanen sune Abdulrazak Umar da aka sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa da aka sani da Yunusa bin Musa, da kuma Shamsu Adamu Sani da ya shahara da Abu Itisar. A ranar 15 ga watan Mayu ne wasu dandazon 'yan bindiga suka kai hari a makarantu guda uku, inda suka yi awon-gaba da ɗalibai da dama…
Read More

Mahaifin marigayiya Habila ya nemi Sufeto-Janar ya ba su gawarta don jana’iza

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tanko Habila, wato mahaifin wannan malamar asibitin da ta rasu a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, Mis Mary Habila, ya yi wa Sufeto-Janar na Rundunar 'Yan sanda ƙorafi, inda ya nemi a ba su gawarta domin yi mata jana'iza. Habila ya bayyana haka ne ga manema labarai jim-kaɗan bayan miƙa takardar ƙorafin a lokacin da yake tare da matarsa, wasu 'yan gidansu da lauyoyinsu a ranar Juma'a. Ya koka akan yadda kusan mako biyu kenan da rasuwar 'yar tasa, Rundunar 'yan sanda a Jihar Ebonyi ba su bayar da gawarta a gare su ba…
Read More

Ana fuskantar ƙarancin fetur yayin da ‘yan kasuwa suka ƙara farashin defo zuwa N1,350 kowace lita

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Akwai yiwuwar a sake fuskantar ƙarancin man fetur, bayan da 'yan kasuwar da ke shigo da fetur suka sanar da ƙarin farashin lita a defo zuwa kusan N1,350. Wannan mataki na iya tilasta wa gidajen mai ƙara farashin da suke sayar wa jama'a, tare da haddasa cinkoso a wasu tashoshin mai matuƙar ba a samu wadatuwarsa ba. Rahotanni sun bayyana cewa masana'antu tuni suka riga suka sanar da 'yan kasuwa batun sabon farashin wanda ake sa ran zai fara aiki daga ranar 17 ga Yuli, lamarin da zai tilasta wa gidajen mai ƙara farashi…
Read More

Ta yi rashin lafiya gabanin rasuwarta, ku tambayi saurayinta – Ministan Ayyuka kan mutuwar ma’aikaciya Habila a gidansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Ayyuka, David Umahi, ya magantu game da mutuwar malamar asibiti, Mary Habila, inda ya ce ta yi fama da wani rashin lafiya gabanin rasuwarta, lamarin da ya tayar da sabon batu akan abin da ya sababba mutuwarta. Umahi ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Alhamis, inda ya ce marigayiyar ta yi aiki da shi na tsawon kusan shekaru uku kuma kamar 'ya take a wajensa da iyalansa. Ya ce, duk wanda yake son ƙarin bayani akan mutuwarta zai iya tuntuɓar saurayinta, wanda ta yi waya da shi…
Read More

An haramta wa’azi da talla a motocin kasuwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Doka za ta fara cin tarar N50,000 ga masu talla ko wa'azi acikin motocin kasuwa yayin Gwamnatin Tarayya ke ƙoƙarin tabbatar da dokar gyare-gyare a dokokin tuƙi a Nijeriya. Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawa ta tabbatar da ƙudirin gyaran Dokar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta 2026, wanda ke neman a ƙarfafa ayyukan hukumar da haramta wasu ayyuka da ka iya ɗauke hankalin direba yayin da yake tuƙi. A yanzu hakan na jiran amincewar shugaban ƙasa domin ganin an aiwatar da dokar a ƙarƙashin kulawar FRSC. Idan aka sanya mata…
Read More

An haramta wa FRSC aiki a titinan gwamnatocin jihohi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Kano, ta haramta wa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) aiki a titinan gwamnatocin jihohi, tana mai cewa babu dokar da ta bata ikon aiki a hanyoyin jihohi ko na ƙananan hukumomi. Kotun ta bayyana wasu harkokin jami'an FRSC a cikin garin Kano a matsayin haramtattu kuma ba bisa doka ba. Haka kuma, kotun ta ce jami'an hukumar suna tauye 'yancin masu zirga-zirga da ababen hawa wajen tsayar da su, ƙalubalantarsu da haifar musu da jinkirin zuwa wajen da suka nufa a hanyoyin da suke mallakar birni ne ba tare…
Read More

El-Rufa’i ya janye ƙorafe-ƙorafe uku bayan ba kotu haƙuri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Lauya mai kare tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Paul Erokoro (SAN), ya ba wa Babbar Kotun Jihar Kaduna haƙuri da kuma neman janye buƙatu guda uku da lauyoyin El-Rufa'i suka shigar a shari'ar rashawa da ake yi akansa. Rahotanni sun bayyana cewa, Erokoro, wanda a kwanan ya zama mai kare El-Rufai, ya kuma ce ya shirya sabon ƙorafi da zai gabatar wa Mai Shari'a Darius Khobo nan da wani ɗan lokaci. Hakan na zuwa ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta zargi lauyoyin tsohon gwamnan da jinkirta fara sauraren shari'ar ta gabatar…
Read More

Babu tiriliyan N210 da ta ɓata daga asusun NNPC – Bala Wunti ga Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Manaja-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Zuba Jari a Man Fetur na Ƙasa (NAPIMS), Alhaji Bala Wunti ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa babu wata hujja a rahoton kuɗi na Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) na 2023 da ke goyon bayan iƙirarin ɓatar Naira tiriliyan 210 daga asusun kamfanin. Da yake jawabi a gaban kwamitin nazari kan kuɗaɗen NNPCL na majalisar, Bala Wunti ya ce ya bi takardar rahoton kuɗaɗen daki-daki yana nazari a kai bayan kwamitin ya buƙaci hakan, yana mai cewa batun tiriliyan 210 kuskuren bin tsare-tsaren shigarwa ne…
Read More