22
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya bayyana Gwamnatin Tarayya na shirin mayar da wasu otel ɗin Zaria (Zaria Hotels) da ke Jihar Kaduna zuwa ajujuwa da kuma ɗakunan kwanan ɗalibai na Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAT). Keyamo ya sanar da samun otel-otel ɗin Zaria a matsayin wani ɓangare na walwalar NCAT, yayin wani rangaɗin sanin makamar aiki a ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri na da nufin bunƙasa cigaban kwalejin. “NCAT ta kasance cibiya mafi kyawu na sufurin jiragen sama a Nijeriya da Afirka ta Yamma. Filin da muke da shi…
