ukarofi

11612 Posts
Kotu ta tsare matar da take ɗaɗara garwashi a al’aurar yarinta

Kotu ta tsare matar da take ɗaɗara garwashi a al’aurar yarinta

Daga MAHD MM. MUHAMMAD Wata Kotun Majistare da ke Abeokuta, reshen Isabo, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wata mata ’yar shekara 25 bisa zargin ta da yi wa wata yarinya 'yar shekara 12 mummunar azaba da wuta ta hanyar ɗaɗara mata a al’aurarta. Wadda ake tuhumar wadda ke zaune a lamba 6 Isewo Dotin a unguwar Obada-Oko a Abeokuta, tana fuskantar tuhuma guda ɗaya da laifin haddasa mummunar ɓarna. Wadda ake tuhumar ta amsa laifin da ake tuhumarta da aikatawa tare da roƙon gafarar kotun. Alƙalin kotun, B.Ɓ. William, ta bada umarnin tsare ta a gidan gyaran…
Read More
Kwastom ta kama katon 2625 na kodin

Kwastom ta kama katon 2625 na kodin

Hukumar Kwastom ta kama katan 2625 na kodin da kuma katan 80 na sildenafil. Kwanturola na Area 11 command da ke Onne jihar Ribas ne ya nuna wa manema labarai waɗannan kayan. Aƙalla kayan zasu yi naira 2, 250,654,000. Yace waɗannan kayan suna da illa sosai ga lafiyar mutane. Ya ƙara da cewa wannan aikin haɗin gwiwa ne tsakanin kwastom da hukumar hana safara da shan miyagun ƙwayoyi. Yace waɗannan abubuwan shigo dasu ya saɓawa dokar da ƙasa ta tanada na shigowa da abubuwa daga wani wuri. Ya rufe da yin godiya ga hukumar hana sha da safara miyagun ƙwayoyi…
Read More
An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

An samu wata hatsaniya a yankin Ojurowo da ke bangaren Eko jihar Legas. Wata mata a ka kama da sata da sayar da ƙananan yara. Jaridar City Round ta rawaito cewa, matar ta saci yaran daga Ijora sannan ta kawo su Eko don ta sayar. A wani faifan video dake yawo a shafin sada zumunta na X, an ga mutane zagaye da wani gini da ake zargin nan wannan matar ke aiwatar da haramtaccen kasuwancin ta. Kamar yadda aka jiyo sautin wani a faifan bidiyon, yana cewa matar ta amsa cewa za ta siyar dasu a kan kuɗi naira 250,000.…
Read More
An gargaɗi al’umma game da amfani da ruwan sama

An gargaɗi al’umma game da amfani da ruwan sama

Daga Ibrahim Hamisu, Kano A yayin da yanayin damina ke ci gaba da kankama, an buƙaci al’ummar jihar Kano da su kula sosai wajen amfani da ruwan sama a wajen sha da sauran ayyukan yau da kullum.Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi gargaɗin a cikin wata sanarwa da ta fito daga sashin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin, Ibrahim Abdullahi, aka raba wa manema labarai, yau juma'a Kwamishinan ya ce lokacin saukar ruwan sama lokaci ne da ke tattare da hatsari na samuwar cutar amai da gudawa wanda…
Read More
Kano: APC ta buƙaci jami’an tsaro su kama Kwankwaso

Kano: APC ta buƙaci jami’an tsaro su kama Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana kalaman da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a matsayin abun takaici. Jam’iyyar ta maka Kwankwaso a kotu domin a kama shi bisa zargin da ya yi na cewar gwamnatin tarayya na yin katsa-landan cikin harkokin Kano. Shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce babu wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa gwamnatin tarayya. Manhaja ta ruwaito yadda Kwankwaso ya yi zargin gwamnatin tarayya ƙarkashin jam’iyyar APC na yunƙurin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar. Kwankwaso,…
Read More
Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karɓar kuɗin fansa miliyan N16

Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karɓar kuɗin fansa miliyan N16

’Yan bindiga sun harbe wani matashi mai shekaru 27 har lahira bayan sun karɓ i kuɗin fansar Naira miliyan 16 da babura uku domin sako shi da wasu mutane tara a Jihar Kaduna. A ranar 16 ga watan Afrilu ’yan bindiga suka kutsa gidaje a uguwar Iya da ke garin Jere inda suka sace mutane tara sannan suka nemi kuɗin fansa Naira miliyan 30. Wani mazaunin garin mai suna Shuaibu Hussaini ya tabbatar wa wakilinmu a wayar tarho ranar Laraba cewa masu garkuwar sun kashe Abba ne a ranar Asabar. Shuaibu ya ce masu garkuwar sun harbe Abba ne a…
Read More
Yadda Gwamnatin Tarayya ta bankaɗo ma’aikatan bogi da suke zaune a ƙasashen waje 

Yadda Gwamnatin Tarayya ta bankaɗo ma’aikatan bogi da suke zaune a ƙasashen waje 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dakta Folasade Yemi-Esan, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, HOCSF, ta ce aikin tantance ma'aikata da ofishinta ya yi kwanan nan, ya bankaɗo ma’aikatan da ke zaune a ƙasashen waje kuma har yanzu suna samun albashi daga Nijeriya. Yemi-Esan ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ta yi da shugabannin kafafen yaɗa labarai a ranar Laraba a Abuja, kasancewar wani ɓ angare na ayyukan bikin Makon Ma’aikata na 2024. Taken bikin na 2024 shi ne 'Koyar da Ƙwararriyar Afirka don Ƙarni na 21: Gina Tsarukan Ilimin Juriya don Ƙarfafa Samun Haɗuwa, Tsawon Rayuwa, Inganci da…
Read More
Jihar Kogi za ta ɗauki mafarauta 1,000 aikin tsaro

Jihar Kogi za ta ɗauki mafarauta 1,000 aikin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin jihar Kogi na shirin ɗaukar 'yan sa-kai 1,050 da zimmar kyautata tsaron jihar da ke tsakiyar Nijeriya. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa an ɗauki matakin ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da buƙatar da gwamnati ta gabatar mata yayin zamanta na ranar Laraba. Tun da farko, Kwamashinan Ƙananan Hukumomi Salami Ozigi-Deedat ya aika wa majalisar wasiƙar neman amincewarta na ɗaukar mafarauta 50 daga kowace ƙaramar hukuma 21 na faɗin jihar. Gwamnatin ta bayyana ƙarancin jami'an tsaro a matsayin babban dalilin ɗaukar mafarautan aiki. Bayan amincewar da suka yi,…
Read More
Sufeton ‘yan sandan Nijeriya ya tura ƙarin dakaru Ribas bayan kisan ɗan sanda

Sufeton ‘yan sandan Nijeriya ya tura ƙarin dakaru Ribas bayan kisan ɗan sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto janar na 'yan sandan Nijeriya ya yi tir da kisan jami'n rundunar da aka yi a jihar Ribas sakamakon rikicin siyasar da ke ci gaba da ruruwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike. Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce IGP Kayode Egbetokun ya bai wa kwamashinan 'yan sandan jihar umarnin tsaurara tsaro don gano waɗanda suka aikata kisan. Sanarwar ta ce an kashe Sufeto Daɓ id Mgbada da kuma wani ɗan sa-kai Samuel Nwigwe a rikicin da ya auku tsakanin magoya ɓ angarorin biyu bayan…
Read More
Maiduguri na cikin birane mafiya tsaro a Nijeriya – Janar Christopher Musa

Maiduguri na cikin birane mafiya tsaro a Nijeriya – Janar Christopher Musa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hafsan Hafsoshin Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ce Maiduguri babban birnin jihar Borno na daga cikin wurare mafiya tsaro a Nijeriya a halin yanzu duk da rikicin Boko Haram da birnin ya yi fama da shi a baya. Janar Musa ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da yake ganawa da shugabannin kafofin yaɗa labarai a Abuja. Ya ce: "Mutane ne kawai suke ganin kamar babu tsaro a Maiduguri, amma birnin na daga cikin waurare mafiya tsaro a ƙasar yanzu haka”. Babban hafsan tsaron na Nijeriya ya ce rundunar sojin ƙasar ta yi…
Read More