22
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Kano ta roƙi jama'a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin sarautar jihar. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano ranar Alhamis. Abdullahi Kiyawa ya nanata ƙudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Kakakin 'yan sandan ya kuma gargaɗi duk wani mai yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan hukuncin kotu ya gaggauta canja tunani. "Tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, rundunar 'yan sanda za…
