21
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto janar na 'yan sandan Nijeriya ya yi tir da kisan jami'n rundunar da aka yi a jihar Ribas sakamakon rikicin siyasar da ke ci gaba da ruruwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike. Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce IGP Kayode Egbetokun ya bai wa kwamashinan 'yan sandan jihar umarnin tsaurara tsaro don gano waɗanda suka aikata kisan. Sanarwar ta ce an kashe Sufeto Daɓ id Mgbada da kuma wani ɗan sa-kai Samuel Nwigwe a rikicin da ya auku tsakanin magoya ɓ angarorin biyu bayan…
