21
Jun
Fitaccen kamfanin tashoshin talabijin na MultiChoice ya miƙa wuya busa caccakar sa da ake yi, inda ya sake rage farashin biyan kuɗin DSTV da masu amfani da GOtV a Nijeriya, biyo bayan umarnin kotu da ta umurce shi da ya dakatar da yunƙurin ƙarin farashin. Duk da cewa kamfanin na ƙasar Afirka ta Kudu ya dage kan ƙalubalantar hukuncin Kotun Kare Masu Sayayya da Gasa Tsakanin Kamfanoni ta Nijeriya a Abuja, MultiChoice ya rage farashi a manhajarsa a ranar Lahadi, 16 ga Yuni, 2024. Bayan rafe farashin, yanzu masu amfani da DSTV za su biya Naira 29,500 maimakon Naira 37,000…
