09
Jun
Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a kan dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai. Kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata, surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana.A makon da ya gabata mun fara kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci gaba da kwararo…
