11
Jun
Ƙungiyar Ƙwadago tace ba za ta koma yajin aiki ba a ranar 11 ga watan Yuni kan tattaunawar ta da gwamnatin tarayya a kan mafi ƙarancin albashi. Shugaban ƙungiyar Ƙwadagon, Joe Ajaero ne ya sanar da haka a wani taron ƙasa da ƙasa a birnin Geneva, Switzerland. Ajaero ya jaddada cewa, alƙaluman suna gaban shugaban ƙasa, don haka ba za su iya tafiya yajin aiki yanzu ba. "Muna jiran mu ji me shugaban ƙasa zai ce sannan mu zauna taron masu ruwa da tsaki a ƙungiyar Ƙwadagon don sanin menene kuma zamuyi a gaba." Sannan Ajaero ya soki wasu gwamnoni…
