22
Jun
Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Asibiitn ƙwararru na jihar Gombe shi ne mafi daɗewar asibiti a fadar jihar da aka gina shi tun kafin samun ‘yancin kan Nijeriya a shekarar 1958, kuma asibitin ya samu canje-canje sosai domin an fara shi ne tun daga matakin dispensary, ya koma cibiyar lafiyar matakin farko Primary Health Center, daga baya ya zama General sannan aka mayar da shi asibitin ƙwararru wato Specialist. Jin ana kukan cewa asibitin yana fama da ƙarancin kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata, wakilinmu ya ziyarci asibiti inda ya zanta da Daraktan Asibitin Dokta Mu’azu Shu’aibu Ishaƙa, don jin…
