31
Jul
Daga RABIU SANUSI a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Bichi, Hon. Hamza Sule Mai Fata, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa aiwatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaba da ya ce suna sauya rayuwar al'ummar jihar ta hanyar zuba jari a fannin ilimi, ƙarfafa mata da kuma rage talauci. Da yake jawabi a wani taron jama'a da aka gudanar a Bichi, Hon. Mai Fata ya bayyana ɗaukar malamai sama da 8,000 aiki a Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya ce wannan mataki zai taimaka matuƙa…
