01
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda hare-haren 'yan ta'adda suka shafa a ƙaramar Hukumar Bungudu da sauran al'ummomin Jihar Zamfara, tare da bayar da umarnin ƙara zafafa ayyukan soja a faɗin yankin Arewa maso Yamma domin dakile ayyukan ta'addanci. A cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ahmed Dan Wudil, ya fitar ranar Lahadi, Dr. Matawalle ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da tsaro duk da ƙaruwar hare-haren da aka samu a wasu sassan yankin…
