ukarofi

12504 Posts
Yadda jami’in leƙen asirin soji ya rasu yana kare iyalansa daga ’yan bindiga a Abuja

Yadda jami’in leƙen asirin soji ya rasu yana kare iyalansa daga ’yan bindiga a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani jami'in leƙen asirin Rundunar Sojin Nijeriya mai muƙamin kanar, Abdussalam A. Ude, ya rasa ransa bayan ya yi gumurzu da wasu 'yan bindiga da suka kai masa hari domin yin garkuwa da shi a gidansa da ke unguwar Kurudu a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Majiyoyi sun ce, marigayin, wanda ɗan asalin Jihar Enugu ne, na daga cikin ƙwararrun jami'an leƙen asirin soji, kuma ana sa ran za a ƙara masa girma zuwa muƙamin Birgediya Janar a shekara mai zuwa. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai masa farmaki ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan…
Read More
Gwamnatina ta farfaɗo da tattalin Nijeriya da inganta rayuwar ’yan Nijeriya – Tinubu

Gwamnatina ta farfaɗo da tattalin Nijeriya da inganta rayuwar ’yan Nijeriya – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa sake fasalin hukumomin tsaro da yadda ake gudanar da ayyukansu zai haifar da gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ta'addanci, 'yan fashi daji da masu garkuwa da mutane a faɗin Nijeriya. Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Taron Manyan Limaman Cocin Katolika na Nijeriya (CBCN) ƙarƙashin jagorancin shugabansa, Archbishop Matthew Ndagoso na Kaduna. Taron ya samu halartar manyan limaman cocin guda 19. Shugaban ƙasar ya ce, gwamnatinsa na sake tsara tsarin…
Read More
Jigawa ta sasanta rikicin gonaki tsakanin Nijeriya da Nijar na shekaru 47

Jigawa ta sasanta rikicin gonaki tsakanin Nijeriya da Nijar na shekaru 47

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kawo ƙarshen rikicin gonaki da ya shafe shekaru 47 yana ci gaba tsakanin al'ummar Jobi da ke ƙaramar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa da kuma al'ummar Kyalli da ke Jamhuriyar Nijar, bayan ƙaddamar da rabon madadin gonaki ga manoman da rikicin ya shafa. Matakin ya biyo bayan aiwatar da shawarwarin da Kwamitin Iyakokin Jihar Jigawa da kuma Hukumar Kula da Iyakokin ƙasa ta Nijeriya (NBC) suka bayar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar…
Read More
Tinubu ya ƙi ganawa da tawagar Ramaphosa kan hare-haren ƙyamar baƙar fata

Tinubu ya ƙi ganawa da tawagar Ramaphosa kan hare-haren ƙyamar baƙar fata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙi karɓar baƙuncin tawaga ta musamman da Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aiko zuwa Nijeriya domin tattaunawa kan hare-haren ƙyamar baƙar fata da ake kai wa 'yan Nijeriya da sauran 'yan Afirka a ƙasar. Maimakon ganawa da tawagar, Shugaba Tinubu ya umarce ta da ta gana da ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, wanda zai gabatar masa da rahoton tattaunawar. Majiyoyi da dama daga Fadar Shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ministan Hulɗar ƙasashen Waje da Haɗin Gwiwa na Afirka ta…
Read More
Idan Gwamna Abba ya yi wa’adi na biyu, Kano za ta samu ninkin ci gaba — Hon. Nura Galadanci

Idan Gwamna Abba ya yi wa’adi na biyu, Kano za ta samu ninkin ci gaba — Hon. Nura Galadanci

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Shugaban Majalisar Kansiloli ta ƙaramar Hukumar Gwale, kuma Kansilan Mazaɓar Galadanci, Hon. Nura Adamu Galadanci, ya bayyana cewa babu wani gwamna da ya gudanar da ayyukan raya Jihar Kano kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa idan aka sake zaɓensa domin wa'adi na biyu, jihar za ta samu ninkin ayyukan ci gaba. Hon. Galadanci ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, inda ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawo sauye-sauye masu yawa a fannoni daban-daban na rayuwar al'umma. Ya ce duk wanda ya kasance a…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe Kanal ɗin sojin Nijeriya yayin ƙoƙarin hana su sace shi da iyalansa a Abuja

‘Yan bindiga sun kashe Kanal ɗin sojin Nijeriya yayin ƙoƙarin hana su sace shi da iyalansa a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani Kanal mai aiki a sashen leƙen asirin Sojin Nijeriya, Abdussalam Ude, ya rasu bayan da wasu ‘yan bindiga suka harbe shi yayin da yake ƙoƙarin hana su sace shi a gidansa da ke unguwar Kurudu a Abuja. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan jami’in ya dawo gida. A cewar PRNigeria, maharan sun buɗe masa wuta ne yayin da yake fitowa daga motarsa, kafin su yi ƙoƙarin yin garkuwa da shi. Sai dai Mista Ude, wanda Kanal ne a rundunar sojin Nijeriya, ya yi ƙoƙarin kare…
Read More
Hisbah ta haramta kayan ‘na gani ina so’ a Sakkwato

Hisbah ta haramta kayan ‘na gani ina so’ a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta sanar da haramta wasu al'adu da ayyukan da ake gudanarwa yayin bukukuwa da shirye-shiryen aure, tana mai cewa sun saɓa wa koyarwar Musulunci da kyawawan ɗabi'u. Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka haramta akwai kayan "Na Gani Ina So" (See I Loɓe), wato al'adar da saurayi ke kai wa iyayen budurwa kayan sha, biskit, alewa, goro da sauran kyaututtuka a lokacin neman aure. Hukumar ta kuma haramta gudanar da sana'ar DJ da kunna waƙoƙin Wazigidi a bukukuwa da tarukan nishaɗi da maza da mata ke…
Read More
Mahara sun kashe mutum 30, ciki har da yara biyar ’yan gida ɗaya a Kaduna

Mahara sun kashe mutum 30, ciki har da yara biyar ’yan gida ɗaya a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aƙalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu, ciki har da ƙananan yara biyar ’yan gida ɗaya, bayan wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai mummunan hari ƙauyen Naridon da ke Gundumar Kamaru Chawai, a ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Litinin, inda maharan suka farmaki ƙauyen, suka kashe mutane da dama, suka jikkata wasu tare da ƙona gidaje masu yawa. Rahotanni sun bayyana cewa yara biyar ɗin, waɗanda dukkansu ’ya’yan wani magidanci mai suna Emmanuel ne, sun rasa rayukansu yayin da iyayensu suka tsallake rijiya…
Read More
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba da sabon ɗakin watsa labarai na zamani na NTA

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba da sabon ɗakin watsa labarai na zamani na NTA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana gamsuwar sa kan sabon ɗakin watsa shirye-shiryen talbijin na zamani da aka kammala a hedikwatar Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), tare da cigaban da aka samu a aikin gyaran Cibiyar ‘Yan Jarida ta ƙasa (National Press Centre). Idris, wanda ya bayyana cewa waɗannan ayyuka hujja ne ƙarara da ke nuna ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na zamanantar da cibiyoyin yaɗa bayanai na gwamnati, ya bayyana haka ne a ranar Litinin bayan ya duba waɗannan cibiyoyi da ke Abuja. A cewar sa, waɗannan…
Read More
ICPC ta kai ƙarar likitan El-Rufai gaban Majalisar Likitoci kan zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na bogi

ICPC ta kai ƙarar likitan El-Rufai gaban Majalisar Likitoci kan zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na bogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta kai ƙarar likitan da ake zargi ya ƙirƙiri rahoton lafiya da aka yi amfani da shi wajen neman belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, gaban Majalisar Likitoci da Likitocin Haƙora ta Nijeriya (MDCN), tana neman a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa. A cikin wata takarda da ta aike wa Kwamitin Binciken Likitoci na MDCN, shugaban ICPC ya nemi a buɗe cikakken bincike kan Farfesa Bello Abubakar, babban ƙwararren likitan cutar daji (Clinical/Radiation Oncologist) da ke aiki a Asibitin ƙasa da ke…
Read More